Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sake Neman Wata Babbar Bukata Bayan Karbar Kudin Fansa Miliyan 10

Kaduna: 'Yan Bindiga Sun Sake Neman Wata Babbar Bukata Bayan Karbar Kudin Fansa Miliyan 10

  • 'Yan bindiga a jihar Kaduna sun bukaci karin babura guda biyu bayan karbar kudin fansa har naira miliyan 10
  • 'Yan bindigan sun sace mutane 23 a ranar 30 ga watan Oktoba a kauyen Kudiri da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna
  • Daga bisani hudu daga cikin wadanda aka kaman sun samu damar kubucewa inda su ka bar mutane 19 a hannunsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Wasu 'yan bindiga sun bukaci babura kirar 'Bajaj' guda biyu bayan karbar kudin fansa naira miliyan 10.

Wannan na zuwa ne bayan sun sace mutane 23 a kauyen Kudiri da ke karamar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Kotu ta daure matashi wata 6 a gidan kaso saboda satar maggi da sabulu, Alkali ya ba shi zabi

'Yan bindiga sun sake neman babbar bukata bayan karbar kudin fansa miliyan 10
Masu garkuwa sun yi tsaurin ido a Kaduna bayan karbar kudin fansa miliyan 10. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Yaushe aka sace mutanen a Kaduna?

Daily Trust ta tattaro cewa 'yan bindigan a ranar 30 ga watan Oktoba sun dira a kauyen inda su ka sace mutane 23 da yaran Fasto guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, hudu daga cikin wadanda aka sacen sun tsere bayan bacci ya sace masu garkuwar.

Daga cikin wadanda ke hannun 'yan bindigan akwai Ayuba Joseph da Josiah Daniel da Fatima Musa da Thomas Iliya da Christopher Yari da Justina Ishaku da Gladys Sarki da Alheri Josiah da Dorcas Daniel.

Wane martani 'yan uwansu su ka yi?

Sauran sun hada da Awaje Daniel da Fada Ishaku da Salvation Yohana da Lucky Thomas da Kamilu Mai Shayi da Sandra Yohana da Hassan Lucky da Fallalu Abubakar da Sharon Thomas da Hannatu Thomas.

Wani daga cikin 'yan uwan wadanda aka kaman, Abdullahi ya ce bayan sun biya miliyan 10 yanzu 'yan bindigan sun zo da wata bukata.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Ya ce sun bukaci dole a siya musu sabbin babura kirar 'Bajaj' guda biyu kafin su sake su, cewar Tori News.

Jerin hare-haren kuskure da soji su ka yi a Najeriya

A wani labarin, tun bayan harin bam a Tudun Biri a jihar Kaduna, an yi ta cece-kuce kan ganganci na jami'an tsaro.

A cikin wannan rahoto, mun jero muku hare-haren da sojin kasar su ka kai kan jama'a wanda su ka ce kuskure ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.