Miyagu Sun Kai Farmaki Makarantar Gwamnatin Tarayya, Sun Tafka Mummunar Ɓarna
- Wasu yan daba sun kutsa kai kwalejin koyon aikin noma ta gwamnatin tarayya da ke Akure (FECA) a jihr Ondo
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun lalata gonakin makarantar da kayan aiki, lamarin da ya haddasa zanga-zanga
- Ma'aikata da ɗaliban kwalejin sun fantsama zanga-zanga suna neman a tsaftace makarantar daga miyagu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akure, jihar Ondo - Wasu tsageru da ake kyautata zaton yan daba ne sun kutsa kai tare da fasa wani sashin katangar kwalejin koyon aikin gona ta tarayya da ke Akure (FECA).
Ƴan daban sun yi amfani da wasu kayan aiki wajen girbe bishiyoyi masu amfani kana suka lalata sashi mai yawa na yankin gonakin makarantar FECA, kamar yadda The Nation ta tattaro.
Atiku da Ɗangote sun lale Naira biliyan uku sun baiwa ɗan takarar gwamna a arewa? Gaskiya ta yi halinta
Zanga-zanga ta ɓarke kan wannan hari
Wannan ɓarna da ƴan barandan suka aikata ta jawo ma'aikata da ɗaliban kwalejin sun fito kan tituna zanga-zanga a Akure, babban birnin jihar Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu zanga-zangar sun buƙaci mahukunta su yi duk mai yiwuwa wajen kawo ƙarshen ɓarnar da ake yi a gonakin da suke mallakin kwalejin noma.
Ma’aikata da daliban da suka fito zanga-zangar sun mamaye ofishin mataimakin sufetan yan sanda (AIG) na shiyya 17, ofishin gwamna da fadar Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Aladelusi Odundun II.
Daga cikin allunan da masu zanga-zamgar ke ɗauke da su an rubuta abubuwa kamar, “Kada ku gurgunta FECA, “A ceci FECA daga masu kwace filaye, “Filin FECA ba na siyarwa bane."
Haka nan wasu allunan an rubuta, “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta kawo agaji kwalejin FECA, “Dan Allah a bar FECA ta numfasa," da sauran makamantan su.
An hana mu koyar da ɗalibai yadda ya kamata - Malami
Shugaban masu zanga-zangar kuma shugaban kungiyar malaman kwalejin (ASUC), Mista Kayode Sule, ya ce ayyukan ‘yan fashin gonaki sun shafi horar da daliban makarantar.
A rahoton Tribune, Sule, wanda ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta shiga tsakani, ya ce:
"Abin da ke faruwa shi ne, mun shiga wata matsala ta ‘yan fashin gonaki waɗanda ke zuwa lokaci bayan lokaci suna damun mu a kwalejin."
"Yanzu da nake magana da ku suna can makarantar suna lalata mana gonaki da kayan aikin da muke horar da ɗalibai."
Yan Bindiga Sun Tarwatsa Mutanen Gari Guda
A wani rahoton kuma Miyagun 'yan bindiga sun kai mummunan harin kauyen Kidandan da ke yankin ƙaramar hukumar Giwa a jihar Kaduna.
Mazauna garin maza da mata da ƙananan yara sun tattara sun bar garin bayan harin wanda yan bindigan suka kashe mutane da yawa.
Asali: Legit.ng