Ku Yi Hattara, Akwai Jabun Kudi Da Ke Yawo": Gargadin CBN Ga 'Yan Najeriya
- Babban bankin Najeriya ya yi gagarumin gargadi ga al'ummar kasar yayin da ake fama da karancin kudi
- Kamar yadda CBN ya bayyana, wasu miyagu na nan suna yada jabun kudi a kasuwannin abinci da sauransu
- CBN ya bukaci yan kasuwa, bankuna da sauransu a kan su yi hattara yayin hada-dabar kudi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Yayin da ake fama da karancin kudi a Najeriya, Babban Bankin kasar ta gargadi yan Najeriya a kan jabun kudade da ke yawo.
Babban bankin kasar ya yi gargadin ne a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Juma'a, 8 ga watan Disamba mai taken "ku yi hattara da jabun kudi da ke yawo".
CBN ya hada kai da jami'an tsaro don kamo masu hannu a yada jabun kudi
CBN ya bukaci dukkan bankuna, wuraren ajiyen kudi, yan canji da sauran jama'a da su kara taka tsantsan tare da daukar duk matakan da suka dace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, babban bankin ya ba da tabbacin cewa yana aiki tare da jami'an tsaro domin kama masu hannu a lamarin.
A cewar bankin:
“An janyo hankalin Babban Bankin Najeriya (CBN) kan yadda wasu mutane ke yawo da jabun takardun kudi, musamman manyan naira domin yin hada-hadar kudi a kasuwannin abinci da sauran cibiyoyin kasuwanci a manyan biranen kasar.
“Don kauce wa shakku, sashi na 20 (4) na dokar CBN (2007) da aka yi wa gyara, ya bayyana cewa: “Zai zama laifin da za a yanke hukuncin zaman gidan yari na abun da ba zai yi kasa da shekaru 5 ga duk mutumin da ya buga jabun takardar kudi da ake amfani da su a Najeriya."
“CBN na ci gaba da hada kai da hukumomin tsaro da na kudi da abin ya shafa domin kwace takardun jabun Naira, tare da kamawa dagurfanar da masu buga kudaden. Ana kuma kara kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargi yana da jabun takardun naira zuwa ofishin yan sanda mafi kusa, ko kuma reshen babban bankin Najeriya.”
"A halin yanzu, ana umurtan dukkan bankuna, gidajen kudi da wuraren chanji da jama'a baki daya da su zamo masu lura da kyau sannan su dauki duk matakan da suka dace don dakile karba da raba jabun kudade."
Babu zancen rufe bankunan yanar gizo
A wani labarin kuma, mun ji cewa hadimin Shugaba Tinubu ta fuskar kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, ya karyata rahoton cewa CBN zai rufe bankunan 'online' irin su Opay, Kuda, Moniepoint, da sauransu.
Hadimin shugaban kasar a shafinsa na Twitter ranar Alhamis ya ce jita-jita ce kawai ake yada wa tare da shawartar jama'a su nemi ilimi kan tsare-tsaren babban bankin don gudun kashe kasuwar bankunan 'online.'
Asali: Legit.ng