“Abin Gwanin Sha’awa:” Malama Ta Bude Wasikar da Dalibarta Ta Rubuta Mata, Ta Cika da Hawaye

“Abin Gwanin Sha’awa:” Malama Ta Bude Wasikar da Dalibarta Ta Rubuta Mata, Ta Cika da Hawaye

  • Wata malamar firamare ta cika da hawaye bayanda ta karanta wasikar da wata dalibarta ta rubuta mata
  • Malamar ta bayyana cewa ta koyar da dalibar ne a zangon karatu na karshe, kuma ta tuno yadda ta lakada wa yarinyar duka don haras da ita
  • A wata hira ta musamman da jaridar Legit, malamar firamaren ta bayyana yadda ta tsinci kanta bayan karanta wasikar dalibar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wata malamar firamare mazauniyar garin Fatakwal mai suna Akie Niibari, ta fito da wata wasika da daya daga cikin dalibanta ta rubua mata.

A wani sako da ta wallafa a sahar Facebook a ranar Juma'a, 1 ga watan Disamba, Akie ta ce ta rasa ta yadda za ta iya saka wa hangen nesan dalibar.

Kara karanta wannan

Ayi hattara: Babbar gadar fita daga Legas ta ruguje, ta haddasa cunkoso

Dalibar firamare ta aike wa malamarta wasika
Aki ta cika da hawaye bayan karanta wasikar da dalibarta ta rubuta mata. Hoto: Akie Niibari
Asali: Facebook

Zuciyarta ta tsuma da irin soyayyar da dalibar ta nuna mata, inda ta Akie ta ce ta koyar da dalibar a zangon karatu na karshe, tare da cewar dalibar na da kokari a karatun ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akie ta wallafa cewa:

"Ta wacce hanya za saka wa wannan dalibar? Wannan soyayyar da me ta yi kama.
"Na samu sako daga wata daliba da na koyar a zangon da ya wuce, yanzu ta na aji hudu kuma tana da kokari. Ni ce malamar ajinsu, gaskiya ina kaunar aikin koyarwar nan."

Daliba ta kyautata wa malamarta

An lankwasa wasikar ta yadda aka rubuta a gefe 'ki bude ta'. A cikin wasikar, dalibar ta bayyana kanta da sunan Chidera kuma tabayyana Akie matsayin malamar da ta fi kauna.

Dalibar ta kuma yi wa Akie murnar shiga sabuwar shekara tare da bukatar ta da ta yi amfani da Naira dari da ke hade da wasikar ta sayi katin waya. Chidera ta ce iya kudin da ta mallaka kenan.

Kara karanta wannan

"Himma ba ta ga rago": Dalibar Najeriya ta yi hijira zuwa turai, ta kama aikin noma gadan-gadan

Akie ta yi karin haske kan dalibarta Chidera

Ko da aka tambaye ta ko akwai wani dalili da ya sa dalibar ta rubuta mata wannan wasikar, Akie ta shaidawa jaridar Legit cewa Chidera ta yi hakan ne kawai don nuna godiya kan kokarin malamar a ilimantar da ita.

Akie ta ce makarantar da ta ke koyarwa ta na a Eleme, Ogale a jihar Rivers.

Akwai soyayya mai karfi tsakanin dalibi da malami

Wani malamin firamare a garin Funtua, jihar Katsina ya shaidawa Legit cewa akwai soyayya mai karfi tsakanin malami da dalibansa, inda wasu ke kuka idan aka zo rabuwa.

Malamin mai suna Yahaya Lawal, ya ce ko shi ta taba faruwa da shi, lokacin yana bautar kasa a wata makarantar sakandire a Dutsinma da ke jihar, sai da kyar aka banbare wata daliba jikinsa a lokacin da zai koma gida bayan kammala bautar kasa.

Kara karanta wannan

"Na gaji da kasar nan": Dirama yayin da yar Najeriya ta nemi kwandastan mota ya kai ta Amurka

Lawal ya ce ma damar malami na koyar da dalibai yadda ya kamata, kuma yana jan su a jiki, to zai samu soyayyar daliban fiye da tunani.

Dan Najeriya ya nemo kamfanin da ke biyan albashin naira miliyan 3 duk wata

Dan Najeriya ya fadi wasu ayyuka guda biyu da mutum zai iya nema wanda ke biyan naira miliyan uku duk wata.

Legit Hausa ta ruwaito cewa kamfanonin dai na aiki ne a Abuja kuma suna neman kwararre da zai kama aiki a guraben da zai samu kudade masu yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.