Ana Tsaka Da Kiran a Tsige Shi, An Gano Wike Yana Rawar Wakar Tinubu a Ofishin Gbajabiamila
- An gano ministan Abuja, Nyesom Wike, yana rera wakar Shugaban kasa Bola Tinubu da taka rawa a ofishin shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila
- Farin cikin da ministan ke nunawa a bidiyon da ya yadu ya zo ne a daidai lokacin da yake fama da rikicin siyasa daban-daban
- Daga cikin rikicin siyasar da Wike ke fuskanta a yanzu harma na neman Shugaban kasa Tinubu ya tsige shi
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - An gano Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya, yana rera wakar Shugaban kasa Bola Tinubu a ofishin shugaban ma'aikatan shugaban kasa.
An gano ministan yana rera shaharariyar wakar nan ta turanci mai taken "Bola, on your mandate we shall stand" cikin yanayi na farin ciki a bidiyon da Legit Hausa ta gani.
Ci gaban na zuwa ne yayin da ministan ke tsaka da fama da rikicin siyasa, ciki harda zanga-zangar da wasu yan Abuja suka yi na neman Shugaban kasa Tinubu ya tsige shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adamu Kabir Matazu, jagoran wata kungiya, ya yi magana a madadin masu zanga-zanga sannan ya yi zargin cewa ya kamata a binciki ministan kan badakalar filaye a Abuja.
Matazu ya yi zargin cewa Birnin tarayya ya zama cibiyar rigima sakamakon matakan da Wike yake dauka, wanda ke kawo karan tsaye ga ajandar Shugaba Tinubu na sabonta fata.
Hakazalika, ministan na fuskantar suka daga sanatar birnin tarayya a majalisar dokokin tarayya, Ireti Kingibe, kan wasu ayyuka da yake gudanarwa.
Kingibe ta bayyana ayyukan a matsayin wadanda basu dace da tsarin rayuwar jama'a ba, ind ta balbale Wike da fada a yayin taron masu ruwa da tsaki don jin ra'ayinta game da ayyukan.
Baya ga rigimarsa da wasu jiga-jigan PDP, tsohon gwamnan na jihar Ribas ya gaza samun zaman lafiya da magajinsa, Siminalayi Fubara, wanda yake zargin ya lalata tsarin siyasar da ya gina.
Kalli bidiyon ministan yana rawa da waka a kasa:
Ana zargin Tinubu a rikicin siyasar Kano
A wani labari na daban, mun ji cewa gamayyar kungiyoyin Arewa a yankin kudu maso yamma ta zargi Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da haddasa rikicin siyasa a jihar Kano.
Kamar yadda jaridar The Guardian ta rahoto a ranar Alhamis, 7 ga watan Disamba, kungiyar ta yi zargin cewa Shugaban kasa Tinubu ne ke da hannu a rikicin da ke faruwa a jihar Kano a kokarinsa na son zarcewa a 2027.
Asali: Legit.ng