Innalillahi: Dan Tsohon Babban Sarki a Najeriya Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Yau Juma’a
- An shiga jimami bayan rasuwar dan marigayi Alaafin na Oyo, Abdulfatai Adeyemi da safiyar yau Juma'a
- Marigayin ya rasu ne bayan fama da jinya ta cutar sukari na tsawon lokaci a yau Juma'a 8 ga watan Disamba
- Marigayin wanda aka fi sani da ‘D-Gov’ ya rasu ne a yau Juma’a kwana daya kafin bikin ranar haihuwarshi shekaru 47
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo – Dan marigayi tsohon Alaafin na Oyo, Prince Abdulfatai Adeyemi ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin wanda aka fi sani da ‘D-Gov’ ya rasu ne a yau Juma’a kwana daya kafin bikin ranar haihuwarshi ta cika shekaru 47, Legit ta tattaro.
Yaushe marigayin ya rasu a jihar Oyo?
Punch ta tattaro cewa marigayin ya rasu ne bayan fama da jinyar ta ciwon sukari a asibitin Jami’ar Ibadan da ke jihar Oyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abdulfatai wanda ya shafe lokaci ya na fama da jinya ya nemi takarar Majalisar Wakilai a jam’iyyar PDP a shekarar 2019, cewar The Nation.
Sai dai marigayin ya rasa damar bayan ya sha kaye a wurin dan uwansa da ke rike da kujerar, Akeem Adeyemi wanda ya koma kujerar karo na biyu.
Wane mukami marigayin ya rike?
Kafin rasuwarshi, Gwamna Seyi Makinde ya nada marigayin a matsayin shugaban hukumar fansho ta kananan hukumomi a wa'adinsa na farko.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar babban alkalin Kotun Daukaka Kara a ranar Laraba 6 ga watan Disamba.
Marigayin, Shagbaor Ikyegh ya rasu kwana daya bayan samun karin girma zuwa Kotun Koli a ranar da ya rasu.
Babban Alkali ya riga mu gidan gaskiya
A wani labarin, Babban alkalin Kotun Daukaka Kara, Mai Shari'a, Shagbaor Ikyegh ya rasu ya na da shekaru 65 a duniya.
Marigayin ya rasu ne da yammacin ranar Laraba 6 ga watan Disamba a birnin Makurdi da ke jihar Benue.
Wannan na zuwa ne kwana daya kacal bayan ya kasance daga cikin wadanda su ka samu karin girma zuwa Kotun Koli a ranar Laraba.
Asali: Legit.ng