CBN Zai Rufe Opay, Moniepoint, Kuda da Sauran Bankunan 'Online'? Hadimin Tinubu Ya Yi Bayani

CBN Zai Rufe Opay, Moniepoint, Kuda da Sauran Bankunan 'Online'? Hadimin Tinubu Ya Yi Bayani

  • Hadimin Shugaba Tinubu ya yi karin haske kan wani rahoto na cewar CBN na shirin rufe Opay, PalmPay, Moniepoint da sauran bankunan 'online'
  • A cewar Dada Olusegun, rahoton kanzon kurege ne tare da yin kira ga jama'a da su rinka yin bincike kafin yada jita-jita da za ta kashe kasuwa
  • A baya ne CBN ya ba da umurnin rufe duk wani asusun ajiyar kudi da ba a makala masa BVN da NIN ba, lamarin da wasu ke ganin zai shafi bankunan 'online'

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Hadimin Shugaba Tinubu ta fuskar kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, ya karyata rahoton cewa CBN zai rufe bankunan 'online' irin su Opay, Kuda, Moniepoint, da sauransu.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna Sani ya caccaki kalaman DHQ kan dalilin jefa bam a taron Musulmai, ya nemi abu 1

Hadimin shugaban kasar a shafinsa na Twitter ranar Alhamis ya ce jita-jita ce kawai ake yada wa tare da shawartar jama'a su nemi ilimi kan tsare-tsaren babban bankin don gudun kashe kasuwar bankunan 'online.'

Opay/Palmpay/Moniepoint/Bola Tinubu/Fadar Shugaban Kasa
Fadar shugaban kasa ta karyata jita-jitar da ke cewa za a rufe Opay, Palmpay, Moniepoint da sauransu. Hoto: Dada Olusegun
Asali: Twitter

A makon da ya gabata babban bankin Najeriya ya ba bankunan ajiyar kudi (DMBs) umurnin rufe duk wani asusun ajiyar kudi da ba shi da BVN da NIN daga shekara mai zuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya sa labarin rufe Opay, Palmpay, Moniepoint ya zama kanzon kurege?

Da yawan bankunan 'online' irin su Opay, Palmpay, da Kuda na ba mutane damar bude asusu ta hanyar amfani da lambar waya kawai, ba tare da sanya BVN ko NIN ba.

Sabanin bankuna na zahiri da sai kana da BVN da NIN, amma bankunan 'online' sun takaita shiga ko fitar kudi akan naira dubu hamsin a asusu mai matakin tsaro na farko.

Kara karanta wannan

Ba a gama da shari'ar zabe ba, Kotu ta rufe asusun bankunan gwamnatin Kano 24 kan dalili 1 tak

Sai dai CBN ya fitar da sanarwar da ke cewa:

"Dole ne duk masu asusun ajiyar kudi da ke da matakin tsaro na farko ya makala BVN da NIN, kamar yadda yake dole masu mataki na biyu da uku su saka BVN da NIN, gaza hakan zai sa a rufe asusun."

Wannan sanarwa ta saka wasu kafofi banda Legit ikirarin cewa babban bankin zai rufe bankunan 'online' saboda masu amfani da su ba sa saka BVN ko NIN a asusun ajiyar su.

Fadar shugaban kasa ta karyata rahoton rufe Opay, Palmpay, Kuda, Moniepoint

Legit ta ruwaito Olusegun a ranar Alhamis, na bukatar jama'a su rinka neman ilimi kan tsare tsaren gwamnati don gudun yada jita-jitar da za ta kashe wa kamfanoni kasuwa.

Duba sanarwarsa a kasa.

NDIC ta lissafa bankuna 20 da suka rushe

A wani labarin, hukumar Inshorar masu ajiyar kudi ta Najeriya (NDIC) ta bayyana sunayen wasu bankuna 20 da suka gaza, sannan za ta biya wadanda suka yi ajiyar kudi a bankunan.

Hukumar ta bayyana cewa masu ajiya, masu bayar da bashi, da masu hannun jari, za su sami karin naira biliyan 16.16 a kudin da za a biya su, Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.