Hanyar duba matsayin lambar NIN daga wayarku ta hannu

Hanyar duba matsayin lambar NIN daga wayarku ta hannu

- Ma;'aikatar sadarwa ta umarci kamfanonin sadarwa su rufe duk wasu layukan waya marasa lambar katin shaidar dan kasa

- Wannan sabon umarni na zuwa ne a daidai lokacin da harkar tsaro ke kara tabarbarewa a Nigeria

- Hukumar bayar da katin shaidar zama dan kasa (NIMC) ta sanar da yadda za'a iya duba matakin lambobin tantancewa

Hukumar bayar da katin shaidar zama dan kasa (NIMC) ta ce za'a san matsayin alaka a tsakanin lambobin tantancewa (NIN) na jikin katin dan kasa da lambar waya.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na tuwita, NIMC ta ce 'yan Nigeria zasu iya sanin ko an hada lambobinsu na NIN da layin wayarsu ta hanyar aika *346# daga layin da aka yi rijista da shi yayin yankar katin shaidar zama dan kasa.

Sannan sai a latsa lamba daya (1) idan an aiko da sakon martani. Lambobin su na aiki a dukkan kamfanonin sadarwa da ke aiki a Nigeria.

KARANTA: An dakatar da shugaban kwalejin kimiyya bayan gano katafaren gado girke a ofishinsa

A ranar Talata ne gwamnatin tarayya ta bada umurni ga dukkan kamfanonin sadarwa su rufe layin wayan duk wanda bai hada layinsa da lambar katin zama dan kasa ba nan da ranar 30 ga Disamba, 2020.

Hanyar duba matsayin lambar NIN daga wayarku ta hannu
Hanyar duba matsayin lambar NIN daga wayarku ta hannu
Asali: Twitter

Wannan umurni ya biyo bayan ganawar gaggawan masu ruwa da tsaki a sashen sadarwa da Minista, Dakta Isa Ibrahim Ali Pantami, ya shirya ranar Litinin, 14 ga Disamba, 2020.

KARANTA: Boko Haram sun kashe wani ango, sun yi amfani da wayarsa wajen sanar cewa "ni dan wuta ne"

Bayan ganawar, an yi ittifakin cewa fari daga ranar Alhamis, 16 ga Disamba, 2020, dukkan kamfanonin sadarwa su bukaci mutane su hada layukan wayansu da lambar katin zama dan kasa.

Gwamnatin tarayya a makon jiya tace an rage kudin 'Data' da kashi 50% bisa umurnin da aka baiwa hukumar sadarwan Najeriya NCC. Saboda haka, kudin 'Data' na 1GB ya sauko daga N1000 zuwa N487 daga yanzu ( tun watan Nuwamba), The Nation ta ruwaito.

'Data' kudi ne da mutum ke saya a domin amfani da samun shiga yanar gizo.

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami, wanda ya sanar da hakan ya ce, an yi hakan ne bisa umurnin da aka baiwa hukumar NCC na tabbatar da cewa an rage kudin 'data' a fadin tarayya.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel