Daya Daga Cikin Alkalan Da Suka Samu Karin Girma Jiya Ya Rasu Ana Kan Tuhumarsa Da Cin Hanci
- Daya daga cikin alkalan da su ka samu karin girma zuwa Kotun Koli ya riga mu gidan gaskiya a jihar Benue
- Marigayin mai suna Shagbaor Ikyegh ya rasu ne a jiya Laraba da yamma kamar yadda iyalansa su ka sanar a yau
- Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne a birnin Makurdi da ke jihar amma ba ta bayyana dalilin mutuwar ba
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Benue - Alkalin Kotun Daukaka Kara da ke jerin wadanda su ka samu karin girma jiya ya ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayin mai suna Shagbaor Ikyegh ya rasu ne a jiya Laraba 6 ga watan Disamba ya na da shekaru 65 a duniya, Legit ta tattaro.
Yaushe marigayin ya rasu a Makurdi?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da iyalansa su ka fitar a yau Alhamis 7 ga watan Disamba a Makurdi babban birnin jihar Benue.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne a birnin Makurdi da ke jihar amma ba ta bayyana dalilin mutuwar tashi ba, cewar TheCable.
Ikyegh na daga cikin alkalan da su ka samu karin girma zuwa Kotun Koli kuma zai yi ritaya ne a shekarar 2028, cewar TheNigeriaLawyer.
Wace sanarwa iyalan marigayin su ka fitar?
Sanarwar ta ce:
"Iyalan marigayin cikin alhini da mika komai ga Ubangiji na sanar da mutuwar danta, dan uwa, miji da kuma uba, Mai Shari'a, Shagbaor Ikyegh.
"Abin takaicin ya faru ne a jiya Laraba 6 ga watan Disamba a birnin Makurdi da ke jihar Benue."
Marigayin ya kammala digiri dinsa a bangaren Shari'a a Jami'ar Obafemi Awolowo, OAU da ke jihar Osun.
Ya fara aiki a Babbar Kotun jihar Benue a shekarar 1991 kafin zuwa Kotun Koli a shekarar 2010.
Shugaban karamar hukumar Gombe ya rasu
A wani labarin, Shugaban karamar hukumar Gombe, Alh Usman Haruna ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da doguwar jinya.
Marigayin da aka fi sani da Ali Ashaka ya rasu ne da yammacin ranar Talata 5 ga watan Disamba a kasar Masar.
Asali: Legit.ng