Sanusi Lamido Ya Caccaki Shugaba Tinubu, Ya Nemi Wani Muhimmin Abu 1
- Sanusi Lamido Sanusi, tsohon gwamnan CBN, ya ce kamata ya yi Shugaba Bola Tinubu ya daina mayar da kansa ministan man fetur
- Tsohon Sarkin Kano wanda tun da farko ya yaba da manufofin Shugaba Tinubu kan tattalin arziƙi, ya buƙaci a binciki kamfanin NNPC yadda ya kamata
- A cewar Khalifan na ƙungiyar Tijjaniyyah, babu bukatar a sake duba dokar CBN don ƴantar da bankin daga harkokin siyasa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanusi Lamido Sanusi, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, ya ce bai kamata shugaban ƙasa ya zama ministan man fetur ba, kamar yadda jaridar Channels tv ta ruwaito.
Ku tuna cewa, a naɗe-naɗen da ya yi, Shugaba Tinubu, ya naɗa ƙaramin ministan man fetur ne kawai, wanda hakan ke nuna cewa zai rike muƙamin ministan man fetur.
Sanusi ya fadi wanda yakamata ya zama ministan man fetur
Naɗa kansa a matsayin ministan man fetur da Tinubu ya yi, ya sa masana harkokin siyasa ke sukarsa, sakamakon yadda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa kansa a matsayin ministan man fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanusi, wanda ya saba tsokaci kan yadda za a magance matsalolin shugabanci a Najeriya, musamman a fannin tattalin arziki, tun da farko ya yaba wa shugaban ƙasar kan manufofinsa na tattalin arziƙi.
Sai dai, da alama bai gamsu da matakin da shugaban ƙasar ya ɗauka na zama ministan man fetur ba.
Tsohon gwamnan na CBN ya kuma yi kira da a yi bincike yadda ya dace a kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), inda ya ƙara da cewa kiran yin hakan da ya yi shi ne ya sa aka cire shi daga mukaminsa na gwamnan CBN.
Sanusi ya buƙaci majalisa ta yi watsi da dokar CBN
Sansi ya riƙe muƙamin gwamnan CBN tsakanin watan Yuni 2009 zuwa Fabrairu 2014 kuma ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake jawabi a taron shugabannin bankin da aka gudanar a dakin taro na Transcorp Hilton da ke Abuja a ranar Alhamis, 7 ga watan Nuwamba.
Tsohon Sarkin na Kano ya kuma ƙara da cewa babu bukatar sake duba dokar CBN domin ƙwato babban bankin daga tasirin siyasa.
Sanusi Ya Yi Tsokaci Kan Tattalin Arzikin Ƙasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya yi magana kan halin da tattalin arziƙin ƙasar nan yake ciki.
Masanin tattalin arzikin yake cewa bashin da gwamnatin Muhammadu Buhari ta rika karba wajen CBN ya taimaka a wajen rusa darajar Naira.
Asali: Legit.ng