Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Yi Wa Jami'an NDLEA Kwanton Bauna, Bidiyo Ya Bayyana
- An yi wa jami’an NDLEA kwanton ɓauna a dajin Opuje da ke ƙaramar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo
- A cewar hukumar yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi a safiyar ranar Alhamis, jami’ai uku sun jikkata yayin harin
- A cikin jami’an da suka jikkata, an yi wa ɗaya daga ciki tiyatar kwakwalwa, amma jami’an sun samu nasarar daƙile harin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Benin, jihar Edo - Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta ce wasu miyagu sun yi wa jami’anta kwanton ɓauna, waɗanda suke kare wani gidan ajiyar miyagun ƙwayoyi a jihar Edo.
A wani sanarwa da hukumar ta NDLEA ta sanya a shafinta na twitter a safiyar ranar Alhamis, 7 ga watan Disamba, hukumar ta ce jami'an sun samu nasarar daƙile harin.
Sanarwar ta ƙara da cewa jami’anta uku sun jikkata yayin da ɗaya ake masa aikin tiyatar kwakwalwa a sashen ICU.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kakakin hukumar, a wata sanarwa a Twitter da ya fitar a ranar Alhamis, ya sanya wani faifan bidiyo na artabu tsakanin jami'an hukumar da ƴan ta’addan, inda ya ƙara da cewa lamarin ya faru ne a dajin Opuje da ke ƙaramar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo.
Sanarwar na cewa:
"A daidai lokacin da jami'an @ndlea_nigeria suka fuskanci wani harin bindiga a wani harin kwanton ɓauna da wasu ƴan bindiga da ke kare wuraren ajiyar miyagun ƙwayoyi suka yi a dajin Opuje da ke jihar Edo."
"Jami'an mu sun samu nasarar fatattakarsu bayan shafe sa'o'i biyu ana fafatawa, uku daga cikin jami'an mu sun samu munanan raunuka, ɗaya an yi masa tiyata a ƙwaƙwalwa."
An gabatar da diyar Tinubu a matsayin sarauniyar Najeriya a wajen bikin daurin aure, bidiyon ya yadu
Ku kalli bidiyon a nan ƙasa:
An Cafke Hatsabibin Dillalin Miyagun Ƙwayoyi
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an hukumar NDLEA sun samu nasarar cafke wani hatsabibin dillalin miyagun ƙwayoyi a birnin tarayya Abuja.
Mai laifin, Ibrahim Momoh, wanda aka fi sani da Ibrahim Bendel, shekaru bakwai da suka gabata ya tsere daga gidan yari bayan samunsa da laifin safarar ƙwayoyi.
Asali: Legit.ng