“Ku Daina Auren Talakawan Mata da Ba Za Su Iya Ba Ku Kudi ba": Daddy Freeze Ya Shawarci Maza

“Ku Daina Auren Talakawan Mata da Ba Za Su Iya Ba Ku Kudi ba": Daddy Freeze Ya Shawarci Maza

  • Wani sanannen mai fadi a ji a dandalin sada zumunta, Daddy Freeze ya yi wani martani mai cike da takaddama kan zamantakewar aure
  • Daddy Freeze ya saki wani bidiyo inda ya bukaci maza da su fara karbar alawus daga wajen matayensu sannan su tambayi me za su iya yi masu
  • Wannan shawara ta sa ta haddasa cece-kuce tsakanin yan Najeriya musamman maza wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Shararren mai fadi a ji a dandalin sada zumunta, Ifedayo Olarinde wanda aka fi sani da Daddy Freeze, ya ba maza wata shawara kan zamantakewa.

Sanannen mutumin ya saki wani bidiyo a shafinsa na Instagram inda ya fada ma maza cewa su fara karbar kudade daga hannun matayensu.

Kara karanta wannan

"Sun yi zaton damfara nake yi": Mai aiki a gidan mai ta dau wanka ta bayan aiki, bidiyon ya yadu

Daddy Freeze ya shawarci maza da su fara karbar kudi hannun mata
“Kada Ku Auri Macen da Ba Za Ta Iya Biyanku Alawus Ba”: Daddy Freeze Ya Shawarci Maza Hoto: @daddyfreeze
Asali: Instagram

A cikin bidiyon, Freeze ya bayyana karara cewa maza na bukatar tashi tsaye kan matan da suka zabi yin rayuwa da su yayin da ya lissafa wasu abubuwa da ya zama dole mace ta mallaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, ya kamata maza su daina auren mata masu yunwa a tare da su sannan su koma bin mata da ka iya biyansu alawus duk wata da yi masu wasu abubuwan.

Da yake ci gaba da magana, ya kara da cewar macen da ba za ta iya yin wannan ba bata cancanci namiji ya bata lokacinsa a kanta ba. Ya ce:

"Ku daina auren mata masu yunwa, wannan ita ce karin bayani ga maza, ya isa haka. Ka aure yarinya sannan ka fada mata 'me za ki iya yi mani? Ku fara samun karfin gwiwa. Nawa za ki dunga biyana a matsayin alawus duk wata? Idan baka hadu da mace da za ta iya biyanka alawus duk wata ba bata cancanci lokacinka ba, ku dina auren na kasa da ku."

Kara karanta wannan

"Zai shafe watanni 4:" Kotu ta tura wani matashi magarkama saboda satar doya a Abuja

Dalilin da yasa bai kamata maza su auri na kasa ba

Domin bayyana abun da yake nufi, Daddy Freeze ya ci gaba da magana kan yadda yaran masu kudi ke auren na sama. Ya ambaci Adenuga, Dangote da Abacha da kuma yadda yaransu duk suka auri masu hannu da shuni.

Sannan ya ce duba ga wadannan, amma wasu mazan sai su je su auri matan da ke karban abun da bai kai nasu ba. Kalamansa:

"Sannan sai kai cikakken namiji, kana zuwa auren wacce ke karbar rabin albashinka ko take fafutukar samu daga abun da kake karba. Yayin da kake karbar 10k duk wata, ka dunga neman macen da ke karbar 30k duk wata kuma dole ta zama kyakkyawa, ta zama mai dirin jiki, ta kware a kan gado. Yadda suke kimanta mu kenan yanzu?"

A karshe Daddy Freeze ya ce:

"Duk macen da ba za ta iya baka alawus a wata ba bata cancanta ba, ku dai bibiyar mata masu yunwa, ku zamo masu aji. Ku daina auren matan da ke da yunwa."

Kara karanta wannan

Zargin maita: Yan sanda sun kama mutum 2 kan kashe dan uwansu da yunwa a Nasarawa

Kalli bidiyon a kasa:

Daddy Freeze ya shawarci mata kan mazan aure

A wani labarin, mun ji cewa wani sanannen mai fada a ji a kafafen sadarwa na zamani, kuma mai watsa labarai mai suna Daddy Freeze ya bayyana alamun da mace za ta gane namijin da ya dace ta aura.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Daddy Freeze ya ce duk namijin da ya sanar da budurwarsa cewa yana da niyyar siya wa mahaifiyarsa mota kafin ita kafin su yi aure, bai cancanci budurwar ta amince ta aure shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng