Kada Mace Ta Kuskura Ta Auri Namijin Da Zai Fara Siya Wa Mahaifiyarsa Mota Kafin Ita, Daddy Freeze

Kada Mace Ta Kuskura Ta Auri Namijin Da Zai Fara Siya Wa Mahaifiyarsa Mota Kafin Ita, Daddy Freeze

  • Wani sanannen mai fadi a ji a dandalin sada zumunta, Daddy Freeze ya bayyana wa mata alamu da suffofin da ya kamata su duba kafin su zabi mijin aure sannan ya basu shawarwari
  • Daddy Freeze ya ce duk namijin da ya sanar da budurwarsa kafin aure cewa sai ya fara siya wa mahaifiyarsa mota kafin ya siya mata, bai cancanci ta aure shi ba
  • Fitaccen mutumin mai shekaru 45 ya ce duk namijin da zai bar matarsa da ciki tana tafiya da kafarta, yayin da mahaifiyarsa tke murza mota, ba mijin aure bane

Wani sanannen fada a ji a kafafen sadarwa na zamani, kuma mai watsa labarai mai suna Daddy Freeze ya bayyana alamun da mace za ta gane namijin da ya dace ta aura.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Daddy Freeze ya ce duk namijin da ya sanar da budurwarsa cewa yana da niyyar siya wa mahaifiyarsa mota kafin ita kafin su yi aure, bai cancanci budurwar ta amince ta aure shi ba.

Kara karanta wannan

Taliban ta haramta kida a Afghanistan, an sanya wa mata sabuwar doka

Kada Mace Ta Kuskura Ta Auri Namijin Da Zai Fara Siya Wa Mahaifiyarsa Mota Kafin Ita, Daddy Freeze
Kada Mace Ta Kuskura Ta Auri Namijin Da Zai Fara Siya Wa Mahaifiyarsa Mota Kafin Ita, Daddy Freeze. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Dadd Freeze ya kula da cewa matsawar namiji ya yi aure, ya fi dacewa ya fifita bukatun matarsa da yaransa kafin na kowa, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda matashin mai shekaru 45 ya ce, duk namijin da zai iya siya wa mahaifiyarsa mota kafin matarsa mai ciki bai cancanci a aure shi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi wallafar ne a yanar gizo tare da wallafa wani hotonsa kafin ya rubuta:

Ya ku matan Najeriya.... kafin ku amince da auren mutum, zai fi dacewa ku yi masa tambayoyi a dabarance don ki gane yanayin tunaninsa. Kamar kice masa, “Idan mun yi aure, wa zaka fara siya wa mota, ni ko mahaifiyarka?’
In dai har yace miki zai fara siya wa mahaifiyarsa, TSERE!”
Duk namijin da zai bar matarsa da ciki tana tafe a kasa, yayin da mahaifiyarsa take murza mota, a tunani na bai cancanci a aure shi ba.”

Kara karanta wannan

Ba boye-boye: Mu ‘yan siyasa ne muka jefa kasar a cikin matsala – Rochas Okorocha

Ya kara da janyo wata aya wacce ya wallafa kamar haka: 1st Timothy 5:8 ta umarci duk wani mai imani a kan ya fara kulawa da iyalansa na farko, mahaifiyarka iyalinka ta nesa ce, matar ka da yaran ka ne iyalan ka na kusa; don haka bukatunsu za ka fara fifitawa!

Aya ta 13:22 tana cewa ya kamata iyayenmu su bar mana gado wanda zai kai har kan jikokinmu, ba wai mu bar musu ba!

Kano: An Saka Dokar Haramta Zancen Dare Tsakanin Samari Da Ƴan Mata a Wata Ƙaramar Hukuma

A wani labari na daban, karamar hukumar Rano a Jihar Kano, a ranar Laraba ta amince da kafa dokar hana tadi ko haduwa tsakanin samari da 'yan mata da dare a jihar, Premium Times ta ruwaito.

Karamar hukumar ta ce an saka wannan dokar ne saboda samun yaduwar badala da ake aikatawa tsakanin samari da yan mata har ma da zaurawa a yankin.

Kara karanta wannan

Sabanin saki cikin fushi, ma'aurata sun yi shagalin rabuwa da juna cikin farin ciki

A cewar rahoton na Premium Times, karamar hukumar ta ce daga yanzu masoya suna iya haduwa ne kawai da rana domin yin tadi.

A cewar jami'in watsa labarai na karamar hukumar, Habibu Faragai, shugaban karamar hukumar, Dahiru Muhammad, ya sanar da dokar ne yayin taron tsaro da masu sarautun gargajiya da mazauna garin suka hallarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel