Tudun Biri: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Magana Kan Kisan Musulmai a Kaduna

Tudun Biri: Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Ya Yi Magana Kan Kisan Musulmai a Kaduna

  • Sanata Barau Jibrin ya yi ta'aziyya ga dangin waɗanda harin bam ɗin sojoji ya shafa a kauyen Tudun Biri a jihar Kaduna
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bukaci a gudanar da bincike mai zurfi kamar yadda Bola Tinubu ya bada umarni
  • Ya kuma yi addu'ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka mutu, ya sa aljanna ta zama makomarsu ta ƙarshe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin, ya mika sakon ta'aziyya dangane da kisan Musulmai a wurin Maulidi a jihar Kaduna.

Sanata Barau ya jajanta wa dangin waɗanda suka mutu a harin bam ɗin da sojojin Najeriya suka kai ƙauyen Tudun Biri, ƙaramar hukumar Igabi ranar Lahadi da daddare.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Ƙungiyar kare hakkin Musulmai ta maida zazzafan martanin kan kisan masu bikin Maulidi

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin.
Tudun Biri: Sanata Barau Ya Yi Ta'aziyya Ga Dangin Waɗanda Suka Mutu a Wurin Maulidi Hoto: Senator Barau Jibrin
Asali: Facebook

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bayyana ruwan bama-bamai kan masu bikin Maulidin da babban abin takaici da nadama, kamar yadda The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Barau ya nemi a gudanar da bincike

Barau ya kuma yi kira da a gaggauta gudanar da bincike mai zurfi kan mummunan ibtila'in kamar yadda Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ba da umarni.

Sanatan ya roƙi hukumomin tsaron Najeriya su kara nazari kan wannan lamarin, wanda a yanzu haka ya yi ajalin rayukan mutane sama da 120, wasu na kwance suna jinya.

Bayan haka Barau ya roƙi ƴan uwan waɗanda wannan hari ya shafa da sauran al'umna mazauna jihar Kaduna su kwantar da hankalinsu su zauna lafiya.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ismail Mudashir, ya fitar ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Sanata ya faɗi matakin da zasu ɗauka domin tabbatar da adalci kan kisan masu Maulidi

Ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu ya ba su Jannatul Firdaus, ya kuma baiwa iyalansu ikon jure wannan baban rashi da suka yi.

Sanata Barau ya ce:

"A wannan lokaci mai wahala, ina tare da iyalan waɗanda abin ya shafa da sauran al'umma. Ina tabbatar musu cewa zan yi iya bakin kokarina wajen tallafa musu da kare faruwar irin haka nan gaba."
"Ina addu'ar Allah ya bai wa sauran waɗanda suka jikkata lafiya yayin da suke kwance a asibiti ana masu magani."

Kungiyoyin arewa sun roki kotun koli ta yi adalci

A wani rahoton kuma Wasu kungiyoyin arewa sun bayyana hukuncin da ya kamata kotun koli ta yanke kan nasarar gwamnonin Kano, Zamfara da Filato.

A cewar shugaban gamayyar ƙungiyoyin, ya kamata kotun koli ta tabbatar da zaɓin da talakawa suka yi a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262