Innalillahi: Allah Ya Yi Wa Shugaban Karamar Hukumar Gombe Rasuwa da Yammacin Yau

Innalillahi: Allah Ya Yi Wa Shugaban Karamar Hukumar Gombe Rasuwa da Yammacin Yau

  • Ana cikin jimami a birnin Gombe bayan rasuwar shugaban karamar hukumar da yammacin yau Talata
  • Marigayin mai suna Alhaji Aliyu Usman wanda aka fi sani da 'Ali Ashaka' ya rasu a kasar Masar bayan fama da jinya
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar kan wannan rashi da aka yi

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - A yammacin yau aka samu mummunan labarin rasuwar shugaban kasarar Gombe, Alhaji Aliyu Usman Haruna.

Marigayin wanda aka fi sani da 'Ali Ashaka' ya rasu ne da yammacin yau Talata 5 ga watan Disamba.

Shugaban karamar hukumar Gombe ya riga mu gidan gaskiya
Marigayin ya rasu ne a yau Talata a kasar Masar. Hoto: Alh Usman Haruna/Facebook.
Asali: Facebook

Yaushe marigayin ya rasu?

Rahoranni sun tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a kasar Masar bayan fama da jinya na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Wakilan Gwamnatin Kaduna sun dira garin da sojoji Suka kashe bayin Allah a taron Maulidi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin, Ali Ashaka ya rasu ya na da shekaru 58 a duniya inda ya bar iyalai da dama.

An haifi marigayin ne a ranar 2 ga watan Yuni na shekarar 1965 wanda ya rasu ya bar mata biyu da ‘ya’ya 16, Tribune ta tattaro.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya yi jimamin rasuwar marigayin.

Wane martani gwamnatin jihar ta yi?

Babban daraktan yada labaran Gwamnan Jihar Gombe, Isma'ila Uba Misilli shi ya bayyana haka a yau Talata 5 ga watan Disamba a cikin wata sanarwa.

Ya ce gwamnan ya samu labarin rasuwar Alhaji Haruna cikin tsananin bakin ciki da damuwa inda ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi.

Ya ce:

“Yayin da muke alhinin wannan babban rashi, muna addu’ar Allah ya gafarta masa kura-kuransa, ya saka masa da Aljannar Firdausi”.

Kara karanta wannan

Harin bam a Kaduna: Mun yi takaici, shugaban sojoji ya roki afuwa kan kisan mutum 85

Kansilar Unguwar Dawaki, Hon Hauwa Saraki ta bayyana kaduwarta kan wannan babban rashi.

Ta bayyana marigayin a matsayin dattijo mai magana daya wanda ba ya saba alkawari.

A cewarta:

"Alhaji Ali Ashaka dattijo ne mutumin kirki mai magana daya, shi ko lokaci aka saka baya ketarewa.
"Ya na daga cikin abin da na koya a wajensa rashin saba lokaci idan zai yi abu zai fito yace zai yi idan ba zai yi ba, ba zai taba fada zai yi ba."

Har ila yau, hadimin Gwamna Inuwa a bangaren yada labarai ta zamani, Yusuf Alyusra ya yi tsokaci kan mutuwar marigayin.

Ya ce mai girma Gwamna da al'ummar jihar sun kadu matuka da wannan babbar rashi.

A karshe, a madadin Gwamna Inuwa da sauran al'ummar jihar Gombe ya yi addu'ar ubangiji ya masa rahama ya saka shi gidan Aljanna Firdausi.

Imam Sa'idu ya riga mu gidan gaskiya a Gombe

A wani labarin, Allah ya karbi rayuwar babban malamin addinin Musulunci a jihar Gombe.

Marigayin, Imam Sa'idu Abubakar kafin rasuwarshi shi ne babban limamin masallacin Abuja Low Coast da ke jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.