Wata Sabuwa: Jam'iyyar Labour Party Ta Caccaki Peter Obi, Bayanai Sun Fito
- Lamidi Apapa, shugaban tsagin jam’iyyar Labour Party (LP) da tawagarsa sun fitar da wata sanarwa inda suka yi kakkausar suka ga Peter Obi
- Tsagin na LP dai sun yi nuni da cewa Obi ya riƙa sukar shugaban ƙasa Bola Tinubu da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba gaira ba dalili
- Don haka tsagin na Apapa, ya nesanta kansa daga “kalaman Obi” waɗanda suka kira a matsayin yaudarar ƴan Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsagin Bashiru Lamidi Apapa na jam'iyyar Labour Party (LP) ya bayyana Peter Obi a matsayin "shugaban ƴan adawa mai cike da haushi".
Peter Obi dai tsohon gwamnan jihar Anambra ne kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar LP a zaɓen 2023 a Najeriya.
'Har yanzu Obi yana ƙarya', tsagin LP
Tun bayan da ya sha kaye a kotun ƙoli a watan Oktoba, ya sha alwashin yin aikin ƴan adawa yadda ya kamata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa a ranar Talata, 5 ga watan Disamba, mai magana da yawun tsagin LP, Abayomi Arabambi, ya soki Obi bisa cigaba da yin Allah wadai da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu, jaridar The Punch ta ruwaito.
Arabambi ya ƙara da cewa Obi ya kasance "mara son kishin ƙasa wanda baya son ganin ƙasar nan ta cigaba."
A cewar Arabambi, Apapa baya goyan bayan "maganganun rashin kan gadon" da Peter Obi ke yi.
Ya ce Obi ya kasance “sananne wajen ƙirƙiro bayanan ƙarya don yaudarar ƴan Najeriya masu kishin ƙasa”.
Apapa ya caccaki Peter Obi
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"An gano cewa bayanan da Peter Obi ya ambato ƙarairayi ne kawai na mai kiran kansa shugaban ƴan adawa waɗanda babu kishin ƙasa da fatan alheri ga ƙasar nan a tattare da shi."
"Daga cikin rahoton ƙididdigar bauta na 2023 na Walk Free Organisation, ƙasar da take da yawan mutanen da suke fuskantar bauta a 2023 ita ce Koriya ta Arewa."
"Don haka, Peter Obi ya kamata ya riƙa bincike kafin ya fito gaban mutane ya riƙa bayar da bayanan ƙarya."
"A Afirika ƙasashen da suke da yawan bauta sune Eritrea, Mauritania da South Sudan. Najeriya an sanya ta cikin ƙasashen da babu bauta sosai a cikinta."
Arabambi ya ƙara da cewa:
"Don haka shugaban LP na ƙasa Alh Bashiru Lamidi Apapa ya nesanta jam’iyyar daga maganganun rashin kan gado na Peter Obi, wanda ya shahara wajen ƙirƙirar alƙaluma, bayanai don yaudarar ƴan Najeriya marasa kishin ƙasa da magoya bayansa masu nuna ƙabilanci ƴan Obidients."
Peter Obi Ya Yabi Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya aike da saƙon taya murna ga Atiku Abubakar.
Obi a saƙon taya murnar da ya aike ya yabi Atiku wanda ya bayyana a matsayin babban yaya kuma jagora.
Asali: Legit.ng