Yayin da Ake Jimamin Hari Kan Masu Maulidi, Dan Majalisa Ya Kaddamar da Shirin Kulawar Lafiya Kyauta
- Yayin da ake cikin jimamin mutuwar mutane masu Maulidi a Kaduna, dan Majalisa ya kaddamar da shirin ba da kulawar lafiya kyauta a jihar
- Dan Majalisar mai suna Mista Daniel Amos ya ce ya kaddamar da shirin ne don taimakon masu karamin karfi musamman a yankinsa
- Amos shi ne dan Majalisar Wakilai da ke wakiltar mazabar Jama’a/Sanga da ke jihar Kaduna a Majalisar Tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kaduna - Akalla mutane fiye da dubu daya ne su ka samu kulawar lafiya kyauta wanda aka shafe tsawon kwanaki biyar ana yi a jihar Kaduna.
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Jama’a/Sanga a jihar Kaduna, Mista Amos Daniel shi ya dauki wannan nauyi don taimaka wa al’umma.
A ina aka kaddamar da shirin?
An kaddamar da shirin ne a asibitin Marigayi Patrick Yakowa a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jama’a da ke jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yayin kaddamarwar, Mista Daniel ya ce ya shirya wannan ba da kulawar lafiyar ce don taimakon al’umma musamman marasa karfi.
Amos ya ce zuba hannun jari a harkar lafiya da ilimi ba iya daidaikun mutane zai amfana ba, har da al’umma gaba daya, cewar Tribune.
Ya ce wannan shiri na daga cikin kokarin sanya farin ciki a zukatan al’ummar yankinsa musamman wadanda ba su da karfi.
Wane alkawari Daniel ya dauka?
Ya ce:
“Samar da kulawar lafiya kyauta a yau na daga cikin shirye-shirye na don faranta wa wadanda ke fama da matsalolin lafiya a yanki na.
“Mutane da daman a fama da cututtuka amma rashin abin hannu ya sa su ke rasa rayuwarsu, wannan ne dalilin samar da tallafin kyauta ga mutane.”
Dan Majalisar ya ba su tabbacin ci gaba da ba da wannan kular lafiyar kyauta har tsawon rayuwarsa, cewar DayBreak.
Atiku ya yi Allah wadai da harin bam kan masu Maulidi
A wani labarin, Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi Allah wadai da harin bam kan masu Maulidi da aka kai a jihar Kaduna.
Atiku ya bukaci yin binciken gaggawa don sanin ainihin dalilin hakan da kuma samar da hanyoyin kare faruwar hakan a gaba.
Asali: Legit.ng