“Zai Shafe Watanni 4”: Kotu Ta Tura Wani Matashi Magarkama Saboda Satar Doya a Abuja

“Zai Shafe Watanni 4”: Kotu Ta Tura Wani Matashi Magarkama Saboda Satar Doya a Abuja

  • Alkalin kotu mai lamba daya da ke Dei-Dei Abuja ya hukunta wani matashi dan shekaru 22
  • Mai shari’a Saminu Suleiman ya yankewa Felix Adams daurin watanni hudu a gidan gyara hali saboda satar doya
  • Da yake ba shi zabin biyan tara N10,000 alkalin ya bukaci wanda aka hukuntan da ya guje ma sake aikata laifi a gaba bayan ya kammala wa'adinsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Abuja - Wata kotu mai lamba 1 a yankin Dei-Dei, Abuja ta yankewa wani matashi mai shekaru 22, Felix Adams, daurin watanni hudu a magarkama saboda satar doya a gonar wata makaranta.

An tuhumi Adams wanda ba a bayyana adireshin sa ba da laifin zamba da kuma sata, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya tsokano Rigima da ikirarin babu aikin da Buhari ya yi a shekara 8

An yankewa matashi hukuncin watanni 4 a magarkama kan satar doya
“Zai Shafe Watanni”: Kotu Ta Tura Wani Matashi Magarkama Saboda Satar Doya a Abuja Hoto: Court of appeal
Asali: UGC

Mai gabatar da kara, Mista Chinedu Ogada, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 19 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kama mai laifin

Ogada ya bayyana cewa tawagar yan sanda da ke fatrol, karkashin jagorancin Misata Tonushi Chibwa, sun kama mutumin yayin da suke aikin sintiri sannan suka kai shi ofishin yan sanda da ke Dutse Alhaji a wannan rana.

Ya bayyana cewa a wannan rana da misalin karfe 10:00 na dare, tawagar fatron din sun kama mai laifin da doya da ake zargin ya sace ne.

Har wayau, ya ce yayin da yan sanda ke bincike da yi masa tambayoyi, mai laifin ya bayyana cewa ya saci doyan ne a wata gona a makarantar sakandare na gwamnati, Dutse Alhaji.

Ya kuma bayyana wa kotun cewa mai laifin ya ce ya saci doyan ne da nufin sayar da su amma a cikin haka ne aka kama shi.

Kara karanta wannan

Zargin maita: Yan sanda sun kama mutum 2 kan kashe dan uwansu da yunwa a Nasarawa

Ogada ya ce laifin ya ci karo da sashi na 348 da 287 na kundin laifuffuka, rahoton Aminiya.

An ba mai laifin zabin biyan tara

Alkalin kotun, Mai shari’a Saminu Suleiman, ya yanke wa wanda ake kara hukuncin zaman gidan yari na watanni hudu tare da zabin biyan tara na N10,000.

Alkalin ya gargade shi da ya guji aikata laifi nan gaba bayan ya kammala hukuncin.

Masu kudi za su fara bayani

A wani labarin kuma, mun ji cewa rundunar yan sandan jihar Delta ta yi kira ga binciken mutanen da ba za su iya yin bayani mai gamsarwa kan tushen arziki da inda suke samun kudaden shigarsu ba, tana mai cew aya kama a bincike su tare da gurfanar da su a gaban kotu.

Kakakin rundunar, Bright Edafe, ne ya yi wannan kira yayin da yake kira ga yan Najeriya da su dauki binciken arzikin da ba a gamsu da su ba a matsayin matakin kare al’umma daga barazanar garkuwa da mutane, kashe-kashe don kudin asiri, da zamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng