Tinubu Ba Irin Buhari Ba Ne, Igboho Ya Sake Gargadin Fulani Kan Barin Yankin Yarbawa, Ya Yi Bayani

Tinubu Ba Irin Buhari Ba Ne, Igboho Ya Sake Gargadin Fulani Kan Barin Yankin Yarbawa, Ya Yi Bayani

  • Sunday Igboho, mai fafutukar kafa kasar Yarbawa ya gargadi kungiyar Miyetti Allah kan ci gaba da daure wa Fulani gindi
  • Igboho ya ce ya kamata shugabannin kungiyar su gane cewa Shugaba Tinubu ba zai lamunci irin ta'addanci da su ke yi ba
  • Wannan na zuwa ne bayan shugaban kungiyar, Bello Badejo ya yi watsi da wa'adin da Igboho ya ba su a kwanakin baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Osun - Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya sake tura sakon gargadi ga kungiyar Miyetti Allah.

Igboho ya tura gargadin ne ga shugaban kungiyar, Abdullahi Bello Badejo kan watsi da wa'adin da ya bai wa Fulani a yankin.

Igboho ya sake tura gargadi ga kungiyar Miyetti Allah
Igboho ya gargadi Fulani makiyaya kan barin yankin Yarbawa. Hoto: Sunday Igboho.
Asali: Facebook

Mene Igboho ke cewa kan Fulani makiyaya?

Kara karanta wannan

Kisan masu maulidi a Kaduna: Dattawan Arewa sun magantu, sun ba gwamnati sharudda

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Igboho ya fitar a ranar Litinin 4 ga watan Disamba, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai fafutukar ya ce kundin tsarin mulkin kasar bai amince da kashe-kashe da sauran ta'addanci da Fulani ke yi ba a kasar.

Ya ce tsohuwar gwamnatin Buhari ta daure wa hakan gindi inda ya ce Bola Tinubu ba zai lamunci irin wannan rashin imani ba, cewar The Eagle Online.

Ya kuma bayyana Badejo a matsayin mai neman suna inda ya ce kundin tsarin mulki ya bai wa kowa damar zama a kasar amma ba tare da kisa da lalata gonaki ba.

Wane gargadi Igboho ya yi ga Fulani?

Ya ce:

"Ta tabbata Badejo suna ya ke so ganin yadda ya daure wa Fulani Makiyaya gindi da ke kisan jama'a ba kakkautawa da kuntatawa jama'ar kasar.

Kara karanta wannan

"Ban ji dadi ba": Tinubu ya magantu kan kisan masu maulidi a Kaduna, ya bayar da wani umurni

"Hatta a Arewacin Najeriya makiyayan na lalata kayan gona da kisan jama'a, ya kamata su sani Tinubu ba irin Buhari ba ne."

Igboho ya kirayi jami'an tsaro da su yi kokarin kare rayuka musamman na manoma da ke shan bakar wahala a hannun makiyaya.

Igboho ya bai wa Fulani wa'adin barin yankin Yarbawa

A wani labarin, Mai fafutukar kafa kasar Yarbawa, Sunday Igboho ya bai wa Fulani makiyaya wa'adin makwanni biyu da su kwashe nasu ya nasu su bar yankin.

Igboho ya gargadi makiyayayan da su tabbatar sun bi wannan umarni ko su fuskanci fushinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.