FUGUS: Iyayen Ɗaliban Jami'ar Tarayya da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Mamaye Gidan Gwamnati

FUGUS: Iyayen Ɗaliban Jami'ar Tarayya da Aka Yi Garkuwa da Su Sun Mamaye Gidan Gwamnati

  • Iyayen ɗaliban jami'ar tarayya ta Gusau da aka yi garkuwa da su sun mamaye gidan gwamnatin jihar Zamfara
  • Sun lashi takobin ba zasu bar gidan gwamnatin ba har sai gwamna da sauran hukumomin tsaro sun ceto 'ya'yansu
  • A watan Satumba ne wasu yan bindiga suka sace ɗalibai sama da 20 da wasu leburori 10 na jami'ar, an ceto 13 a halin yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Iyayen ɗalibai mata na jami'ar tarayya da ke Gusau (FUGUS) sun gudanar da zanga-zangar lumana a gidan gwamnatin jihar Zamfara.

Iyayen daliban jami'ar Gusau sun mamaye gidan gwamnati.
Iyayen Ɗalibai Mata da Yan Bindiga Suka Sace A FUGUS Sun Yi Zanga-Zanga a Zamfara Hoto: FUGUS
Asali: Facebook

Yayin wannan zanga-zanga, iyayen sun buƙaci a sako musu 'ya'yansu cikin gaggawa kuma ba tare da gindaya wani sharaɗi ba, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da yan sanda suka yi arangama da dalibai masu zanga-zanga a jami'ar ATBU

Sun kuma roƙi Gwamna Dauda Lawal da hukumomin tsaro sun yi duk mai yiwuwa wajen ceto 'ya'yansu cikin ƙoshin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka ɗauke ɗalibai mata a FUGUS

Aƙalla ɗaliban jami'ar 24, leburori 10, ma'aikacin jami'a da ɗiyarsa ɗaya ne 'yan bindigan suka yi awon gaba da su ranar 22 ga watan Satumba, 2023.

Yan ta'adda sun sace ɗalibai da ma'aikatan ne yayin da suka kai farmaki Sabon Gida, garin da ke tattare da gidajen kwanan ɗalibai jami'ar FUGUS musamman mata.

Tun bayan aukuwar wannan lamari zuwa yau, ɗaliban sun shafe sama da kwanaki 70 a tsare a hannun ƴan bindiga.

Amma jami'an tsaro sun samu nasarar ceto ɗalibai 13 da leburori 2 yayin da sauran ke hannun masu garkuwa da mutane har kawo yanzu.

'Ba zamu bar gidan gwamnati ba'

Iyayen da suka fito wannan zanga-zanga sun sha alwashin ba zasu bar gidan gwamnatin Zamfara ba har sai an ceto masu 'ya'yansu daga hannun miyagu.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya sun yi martani yayin da yar sanda ta koma sanya wa matar gwamna dan kunne

A cewarsu, yan bindigan da suka sace ɗaliban sun tuntubi wasu daga cikinsu, amma sharaɗin da suke bayar wa shi ne suna buƙatar su tattauna da gwamnati.

Daya daga cikin iyayen, Hajiya Hajara Zakari daga jihar Neja ta nuna damuwarta kan yadda gwamnati da hukumomin jami’ar suka gaza ceto ‘ya’yansu duk da rokon da aka yi musu.

A cewar ta, iyayen sun gana da hukumomin jami’ar kan lamarin amma ba a yi komai ba, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Tankar mai ta yi bindiga a Legas

A wani rahoton na daban Yayin da ake jimamin abinda ya faru a Kaduna, wata babbar mota ɗauke da man Dizel ta fashe ta kama da wuta a jihar Legas.

Hukumar kashe gobara da ayyukan ceto ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami'an sun shawo kan yanayin da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262