COP28: Gwamnati Ta Saki Jerin Wakilan da Ta Tura Taron Dumamar Yanayi Kasar Dubai

COP28: Gwamnati Ta Saki Jerin Wakilan da Ta Tura Taron Dumamar Yanayi Kasar Dubai

  • Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ce wakilai 442 ne kawai ta dauki nauyin su zuwa taron dumamar yanayi da ke gudana a Dubai
  • A cewar jerin sunayen da gwamnatin ta bayar, sauran mutanen da suka je sun je ne kashin kansu, da suka hada da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki
  • Jerin jadawalin sunayen ya nuna cewa an tura wakilai 32 daga hukumar dumamar yanayi ta kasa, sai ma'aikatar muhalli mutum 34, da wasu ministoci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta bayyana adadin mutanen da ta wakilta zuwa taron dumamar yanayi da ke gudana a Dubai.

A wata sanarwa da jaridar Legit ta ci karo da ita ta nuna cewa wakilan da aka tura sun fito daga gwamnatocin jihohi da tarayya.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ana jimamin kashe bayin Allah a wurin Maulidi, wani abu ya fashe a jihar APC

Shugaba Tinubu/Dubai
COP28: Shugaba Tinubu ya saki sunayen wakilan da gwamnatin tarayya ta tura Dubai. Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Sauran wakilan kuma ba gwamnati ce ta tura su ba, wadanda suka hada da kamfanoni, kungiyoyi, 'yan jarida, makarantu, da sauran su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin wakilan da gwamnati ta tura Dubai

A cewar sanarwar, gwamnatin tarayya ta dauki nauyin wakilai 422 ne, da suka hada da:

  1. Hukumar dumamar yanayi ta kasa - Mutum 32
  2. Ma'aikatar muhalli - Mutum 34
  3. Sauran ma'aikatu - Mutum 167
  4. Fadar shugaban kasa - Mutum 67
  5. Ofishin mataimakin shugaban kasa - Mutum 9
  6. Majalisar dokokin tarayya - Mutum 40
  7. Hukumomin gwamnatin tarayya - Mutum 73

Jam'iyyar PDP da LP sun nemi Tinubu ya fadi sunayen wakilan da aka tura Dubai

Da yawa daga cikin 'yan Najeriya sun kalubalanci gwamnatin tarayya na tura mutane da yawa taron dumamar yanayi da ake yi a Dubai da aka fi sani da COP28.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnati ta yi gwanjon babban otel mallakin jihar Kwara? Gaskiya ta bayyana

Jam'iyyun adawa irin su PDP da LP a baya-bayan nan suka nemi shugaban kasar ya fitar da sunayen wakilan da aka tura zuwa kasar.

PDP da LP sun yi Allah wadai da irin yawan wakilan da aka tura, inda ta bayyana hakan matsayin almubazzaranci la'akari da matsin tattali da kasar ke fama da shi.

Da gaske gwamnati ta yi gwanjon babban otel na jihar Kwara?

A wani labarin na daban, gwamnatin jihar Kwara ta magantu kan jita-jitar da ke yawo na cewar ta yi gwanjon babban otel din jihar, Legit Hausa ta ruwaito.

Gwamnatin ta ce babu wani dalili da zai saka a sayar da otel din kasancewarsa kadarar al'uma, kuma wani abu na alfahari ga jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.