Gwamnan Jihar Arewa Ya Koka Kan Yadda ’Yan Bindiga Suka Kwace Wasu Makarantu a Jiharsa

Gwamnan Jihar Arewa Ya Koka Kan Yadda ’Yan Bindiga Suka Kwace Wasu Makarantu a Jiharsa

  • Gwamnatin jihar Katsina ta doka kan yadda wasu makarantu a jihar suka koma mafakar 'yan ta'adda
  • Gwamnan jihar, Umar Dikko Radda ya ce ayyukan ta'addanci a jihar sun jawo rufe makarantu da dama
  • Sai dai gwamnan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa ta dauki matakan kawo karshen matsalar tsaro a jihar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda ya koka kan yadda 'yan bindiga suka kwace wasu makarantu a jiharsa.

Radda ya bayyana hakan a taron jami'ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) na 7 da 8 da aka hade su a jihar Katsina.

Umar Dikko Radda/Gwamnan Katsina/Jami'ar FUDMA
Gwamna Dikko Radda ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru don dakile ayyukan 'yan ta'addanci a jihar. Hoto: @KatsinaStateNg
Asali: Twitter

Jawabin Dikko Radda kan matsalar tsaro a jihar Katsina

Kara karanta wannan

Ni na fatattaki Shekau da Qaqa, da yanzu Niger ta zama hedikwatar Boko Haram, tsogon gwamna Aliyu

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru don dakile ayyukan 'yan ta'addanci a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Babu ilimi idan babu tsaro.
"Da yawa daga makarantun da ke a garuruwan da 'yan ta'adda suka addaba an rufe su, yanzu sun zama mafakar 'yan ta'adda.
"Wannan ya sa muka kaddamar da kungiyar tsaro ta 'Watch Corps' domin yaki da matsalar tsaro da kuma samar da kyakkyawan yanayi na karatu a jihar.

Gwamnan ya kara da cewa:

"Gwamnatina ta damu matuka da daliban da ke gararamba a gari kuma za su yi aiki tukuru don ganin kowanne dalibi ya koma makaranta.

Ba a iya ilimi ba kawai, gwamnatin Katsina ta mayar da hankali kan fannin noma, kiwon lafiya da walwalar jama'a, sannan mun bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga."

Kara karanta wannan

“Idan ba’a kira ni dan midiya ba ɗan uwarki za’a kira ni” Na hannun daman Ganduje ya wanke budurwa

Abin da yasa Tibunu bai yi jawabi a taron COP28 ba

Legit Hausa ta ruwaito maku cewa an tsara shugabannin kasashe za su gabatar da jawabi a ranar 1 da 2 ga watan Disamba a taron COP28 na wannan shekarar a Dubai.

Shugaba Bola Tinubu ne na 36 a jadawalin shugabannin kasashen da za su gabatar da jawabi a wannan taron, amma har rana ta daya da ta biyu ta wuce shugaban bai yi jawabi ba.

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Tinubu bai gabatar da jawabi ba saboda yakininsa na cewa "aiki a aikace Najeriya ke so ba wai yawan magana ba".

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.