Majalissar Tarayya Ta Shirya Taron Jin Ra’ayin Jama’a Kan Kasafin Kudin 2024
- Rahotanni sun nuna cewa kwamitin kasafin kudi karkashin ofishin kakakin majalisar tarayya ya gudanar da taron jin ra'ayoyi
- Taron wanda ya gudana a Abuja, an shirya shi ne don jin ra'ayoyin jama'a kan kasafin kudin 2024 da shugaba Tinubu ya gabatar
- A makon da ya gabata ne shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar wa zaman hadin guiwa na majalisar dokokin tarayya kasafin shekarar 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - An fara gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'a kan kasafin kudin 2024 da shugaban kasa Tinubu ya gabatarwa majalisar dokokin tarayya a Abuja.
Taron na gudana ne karkashin kwamitin majalisar kan kasafin kudi, da kuma sashen gudanar da taruka, na ofishin kakakin majalisar tarayya.
Su wa suka halarci taron?
Manyan mutane sun samu halartar taron da suka hada da shugaban kwamitin kasafin kudi, Kabir Abubakar da mataimakinsa Iduma Enwo, da tsohon sakataren APC, Iyiola Omisore.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabinsa na maraba, Kabir ya bayyana cewa an shirya taron ne don kara jan 'yan kasa a jiki kan lamuran da suka shafi kasafin kudin kasar, The Punch ta ruwaito.
The Nation ta ruwaito Kabir na cewa:
"Jin ra'ayoyin jama'a ya zama wajibi don ganin an tsaftace tare da mutunta tsare-tsaren da ake yi na ganin an amince da kasafin kudin da shugaban ya gabatar."
Yan bindiga sun kwace wasu makarantu a Katsina - Dikko Radda
A wani labarin, gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda ya koka kan yadda 'yan bindiga suka kwace wasu makarantu a jiharsa.
Radda ya bayyana hakan a taron jami'ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) na 7 da 8 da aka hade su a jihar Katsina, Legit Hausa ta ruwaito.
Abin da Gwamna Radda ya ce kan matsalar tsaro
Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki tukuru don dakile ayyukan 'yan ta'addanci a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.
"Babu ilimi idan babu tsaro.
"Wannan ya sa muka kaddamar da kungiyar tsaro ta 'Watch Corps' domin yaki da matsalar tsaro da kuma samar da kyakkyawan yanayi na karatu a jihar.
Asali: Legit.ng