“Ya Sha Bakar Wahala”: Yadda Mai Aikin Famfo Ya Fita Da ‘First Class’ a Jami’ar Najeriya

“Ya Sha Bakar Wahala”: Yadda Mai Aikin Famfo Ya Fita Da ‘First Class’ a Jami’ar Najeriya

  • An samu labarin wani matashi dan Najeriya da ya kammala jami'ar fasaha ta tarayya da ke Owerri (FUTO) a jihar Imo
  • Matashin mai suna Gabriel Nwachukwu Eze, ya kammala jami'ar da sakamako na matakin farko (First Class)
  • A taron FUTO na 34 da 35, an yaye dalibai 5,091, inda Eze da wasu dalibai 119 suka kammala karatu da sakamako na First Class.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Owerri, Imo state - Gabriel Eze ya kasance dalibin jami'ar fasaha ta tarayya da ke Owerri (FUTO) jihar Imo, inda ya kammata da sakamako darajar farko.

Dan asalin jihar Ebonyi, Eze ya sha bakar wahala kafin kammala karatu, kamar yadda wani Dr Laz Ude Eze ya wallafa labarin a shafinsa na X (da aka fi sani da Twitter).

Kara karanta wannan

Dirama yayin da dan takarar gwamnan PDP ya gagara magana da yarensu, ya nemo mai fassara

Gabriel Nwachukwu Eze
Nazarin rayuwar matashi Gabriel Nwachukwu Eze, mai gayaran famfo da ya kammala jami'a da sakamako darajar farko. Hoto: maazi_ogbonnaya
Asali: Twitter

Gabriel Eze, wanda ya fita jami'ar FUTO's da sakamako darajar farko

Da ya ke labarta tarihin rayuwar Eze, Ude ya ce matashin ya rasa mahaifinsa yana da shekaru bakwai, sai dai saboda jajurcewarsa ya cimma nasara lokacin da ya kai shekaru 23.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma wallafa labarin Eze a shafin X a nan da nan, kamar yadda Legit ta ruwaito.

Dr Ude ya ce:

"Saboda ya dauki nauyin rayuwarsa da karatunsa ya fara aikin gyaran famfo, tare da addu'ar mahaifiyarsa ya samu nasarar kammala sakandire, ya samu sakamako mai kyau.
"A shekarar 2017 ya shiga jami'ar FUTO, inda ya karanci fasahar man fetur, kuma har a lokaci yana ci gaba da aikin gyaran famfo don samun kudin shiga."

Dr Ude ya ci gaba da cewa:

"Duk da aikinsa na gyaran famfo, bai samu nakasu a karatunsa ba, illa ma nasarorin da ya samu tare da kyaututtuka daga NNPC/NAOC/OANDA, FTDF, AGBAMI, da sauran su.

Kara karanta wannan

Bani da katabus: Wanda ya kone takardar digirinsa ya yi bayanin dalilansa na bankawa takardunsa wuta

"A watan Disamba 2023, Eze ya kammala karatun jami'a, inda ya fita da sakamako darajar farko, shugaban jami'ar Farfesa Nnenna Oti ya jinjina wa kokarin Eze a wannan rana."

Gwamatin Tinubu ta yi wa 'yan Najeriya albishir kan wutar lantarki

A wani labarin, gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta sha alwashin kawo karshen duk wasu matsaloli da ke addabar fannin wutar lantarki.

Gwamnatin ta ce kudurin dokar wutar lantarki na 2023 zai tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun more ingantacciyar wutar lantarki, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.