Innalillahi: Mutum 5 Sun Kone Kurmus Wasu Mutum 11 Sun Samu Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Innalillahi: Mutum 5 Sun Kone Kurmus Wasu Mutum 11 Sun Samu Raunuka a Wani Mummunan Hatsarin Mota

  • An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a kan babbar hanyar Calabar zuwa Itu a jihar Akwa Ibom
  • Hukumar kiyayye haɗura ta ƙasa reshen jihar wacce ta tabbatar da aukuwar hatsarin ta ce mutum biyar sun ƙone har lahira a hatsarin
  • A hukumar a cikin wata sanarwa ta kuma tabbatar da cewa wasu mutum 11 sun samu raunuka daban-daban a hatsarin motar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Akwa Ibom- An tabbatar da mutuwar mutum biyar tare da jikkata wasu mutum 11 a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ranar Asabar, a kan babbar hanyar Calabar zuwa Itu a jihar Akwa Ibom

Hatsarin wanda ya auku da misalin ƙarfe 3:00 na rana ya ritsa da wata mota ƙirar Nissan Caravan mai lamba GWB532XY da wata babbar mota ƙirar Mark wacce ba ta da lamba, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Innalilahi: Matafiya 9 sun kone kurmus a wani mummunan hatsarin mota

Mutum biyar sun rasu a hatsarin mota a Cross Rivers
Hatsarin ya salwantar da rayukan mutum biyar Hoto: @FRSCNigeria
Asali: UGC

An bayyana hakan a wata sanarwa da babban kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa reshen jihar Akwa Ibom, Mista Matthew Olonisaye, ya fitar a ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, rahoton Leadership ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me nene ya haddasa hatsarin?

Sanarwar mai ɗauke da sa hannun jami’in wayar da kan jama’a na rundunar, Mista Paul James, ta alaƙanta musabbabin hatsarin da gudun da ya wuce ƙima.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mummunan hatsarin ya auku ne a ranar Asabar, 2 ga watan Disamba 2023, a kan hanyar Itu-Calabar ta Ayadehe da misalin ƙarfe 3:10 na rana."
“Hatsarin ya ritsa da wata mota ƙirar Nissan Caravan mai lamba GWB532XY da wata babbar mota ƙirar Mark da ba ta da lamba."
"Maza 11 da mata biyar ne hatsarin ya ritsa da su, sannan uku daga cikin mata biyar da biyu daga cikin maza 11 da lamarin ya shafa an tabbatar da mutuwarsu, yayin da sauran maza da mata 11 da ke cikin motar suka samu raunuka daban-daban."

Kara karanta wannan

Gobara ta tashi a sakatariyar gwamnatin tarayya, bayanai sun fito

Matafiya Sun Kone a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da wasu matafiya a kan titin hanyar Ogobomosho zuwa Oyo a jihar Oyo.

Mutum tara daga 13 da hatsarin motar ya ritsa da su sun samu raunukan ƙuna daban-daban bayan motarsu ta yi karo da tirela.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng