NPA v Intel: Dalilin Maidawa Tsohon Kamfanin Atiku Kwangila da Tinubu Ya Hau Mulki

NPA v Intel: Dalilin Maidawa Tsohon Kamfanin Atiku Kwangila da Tinubu Ya Hau Mulki

  • Fadar shugaban kasa ta na ganin hukumar NPA tayi kuskure wajen soke kwangilar jigilar da aka ba kamfanin INTEL
  • Sanadiyyar korar kamfanin daga tasoshin ruwa, gwamnatin Bola Tinubu ta gano ana tafka asarar $150m a kowace shekara
  • Shugaba Tinubu wanda ya yi umarni a dawo da kwangilar, ya ce ba shi ya saye hannun jarin da Atiku Abubakar ya saida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi karin haske a game da surutun da ya biyo bayan dawo da kwangilar gwamnati da kamfanin INTEL.

Shekaru uku da soke kwangilar da Najeriya ta ba kamfanin INTEL Nigeria Ltd a tasoshin ruwa, an ji labari an sake shiga yarjejeniya.

Atiku da Tinubu
INTEL: Atiku Abubakar da Bola Tinubu Hoto:Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Dalilin Tinubu na dawo da INTEL

Kara karanta wannan

Tinubu ya siya hannun jarin Atiku na $100m a kamfanin Intels? Fadar shugaban kasa ta yi magana

Bayanin da Segun Dada ya yi, ya nuna soke kwangilar jigilar ta yi sanadiyyar da Najeriya ta rika rasa $150m na kudin shiga a shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ganin yadda ake asarar miliyoyin dalolin kudi, Mai taimakawa shugaban kasa Bola Tinubu ya ce sai aka ga bukatar maido da kwangilar nan.

A 1 ga Satumban 2020, sashen LPD na NPA ta ce an soke kwangilar da aka ba Intels, saboda haka jirage za su rika hulda kai tsaye da hukumar.

Jawabin Hadimin Bola Tinubu

"A dalilin karancin kwarewa da sanin aiki, masu harkar ba su iya yin abin da ake bukata ba, hakan ya yi tasiri wajen kudin shiga ta harkar.
Da shigansa ofis, sabuwar gwamnatin Bola Tinubu ta bukaci jami’an gwamnati su duba batun karancin kudin shiga
Kwangilar da aka soke a 2020 ta na cikin abin da ya sa Najeriya ke asarar $150m a shekara.

Kara karanta wannan

Lauyoyi sama da 200 sun shirya tsaf don tabbatar da Abba Gida-Gida ya yi nasara a kotu

Sulhu ce hanyar da Najeriya ta ke bukata domin samun kudin shiga a wannan lokaci, sai aka amince INTEL ta cigaba da aiki a Nuwamban 2023.

- Segun Dada

Atiku ya saidawa Tinubu hannu jari a INTEL?

Segun Dada ya ce a halin yanzu kamfanin Orleal Investment Group ne su ke da INTEL domin Atiku Abubakar ya saida hannun jarinsa na $100m.

Jawabin da aka yi a Twitter ya kuma tabbatar da cewa Bola Tinubu da ya dawo da wannan tsohuwar kwangila bai da hannun jari a kamfanin.

Jihohi sun samu talaffin NG-Cares

Nasarawa ta samu N13,697,828,496.96 daga cikin ragowar kason tallafin COVID-19 da aka rabawa jihohi 36 a karkashin tsarin NG-Gares.

Abin da aka ba Kuros Ribas a karkashin tsarin shi ne N10,944,747,818.84, sai kuma gwamnatin Zamfara ta tashi da N10,231,055,267.82.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng