Shin Tinubu Ne? Atiku Ya Bayyana Wanda Ya Siyarwa Hannun Jarinsa Na $100m a Kamfanin Intels
- Atiku Abubakar ya ce ba shi da wata alaƙa da kamfanin Integrated Logistic Services Nigeria Limited (Intels)
- Hakan ya biyo bayan rahotannin da ke cewa ya ci gajiyar matakin dawo da kwangilar da aka ƙulla tsakanin Intels da gwamnatin tarayya
- Atiku ya ce ya sayar da hannun jarinsa na Intels, a watan Disamba 2020 ga iyayen kamfanin, Orlean Investment Group, kuma ya bayyana ficewarsa daga kamfanin a watan Janairun 2021
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2023, ya ce ya riga ya fice daga kamfanin Intels don haka ba zai iya cin gajiyar matakin dawo da kwangilar da aka yi tsakanin Intels da FG ba.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta mayarwa kamfanin Intels kwangilar sauke kaya a jirgin ruwa bayan shekaru uku.
Wasu rubuce-rubuce, musamman a WhatsApp, har yanzu suna danganta Intels da Atiku.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya bayyana gaskiya kan siyar da Intels
Har ila yau, wasu rahotanni sun yi iƙirarin cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya sayar da hannun jarinsa na Intels kan miliyoyin daloli ga Shugaba Bola Tinubu.
Sai dai, a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba, Atiku ya jaddada cewa ya sayar da Intels ga kamfanin Orlean Investment Group.
Atiku ya rubuta ya rubuta cewa:
"A watan Janairun 2021, na ba da sanarwar sayar da hannun jarina na Integrated Logistic Services Nigeria Limited (Intels) ga Orlean Investment Group, iyayen kamfanin Intels."
"Sayar da hannun jarin ya fara a shekarar 2018 inda aka kammala a watan Disamba na 2020. Kamfanin Intels ya kuma bayyana wa jama’a ficewata daga kamfanin, ma’ana wani kamfani ne na daban yanzu ya mallaki waɗannan hannun jarin da na sayar."
"Sayar da hannun jarina a kamfanin wanda da ni aka kafa shi bai sauya ba. Haka kuma, babu wata hanya da zan amfana da dawo da kwangilar da gwamnatin tarayya ta ƙwace a hannun Intels."
"Saboda haka batun cewa ina amfana da matakin gwamnatin tarayya na dawo da kwangilar da ke tsakaninta da Intels va gaskiya bane kuma ya kamata a kalle shi a yadda yake: ƙarya."
Dalilin da Ya Hana Atiku Komawa Dubai
A wani labarin kuma, kun ji cewa an bayyana dalilin da ya sanya har yanzu Atiku Abubakar bai koma birnin Dubai da zama ba.
Majiyoyi sun bayyana shirin yin takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ne ya hana Atiku komawa Dubai.
Asali: Legit.ng