Yan Sanda Sun Kama Hadimin Abba Gida-Gida Da Wani Kan Laifi 1 Tak

Yan Sanda Sun Kama Hadimin Abba Gida-Gida Da Wani Kan Laifi 1 Tak

  • Jami'an yan sanda a jihar Kano sun cika hannu da wani Tasiu Al'amin-Roba, hadimin gwamnan jihar
  • Yan sandan sun kuma kama wani Abdulkadir Muhammad bisa zarginsu da karkatar da kayan tallafi a rumbun ajiya da ke Sharada
  • Ana tuhumar wadanda ake zargin da sauyawa buhunan shinkafa da masara sama da 200 buhu sannan suka siyar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Rundunar yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da kama babban mai ba Gwamna Abba Yusuf shawara ta musamman, Tasiu Al'amin-Roba da wani Abdulkadir Muhammad kan zargin karkatar da kayan tallafin jihar.

Kwamishinan yan sandan jihar, Hussaini Gumel, ya fada ma kamfanin dillancin labaran Najeriya a wayar tarho cewa an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kayayyaki a yankin Sharada, tare da buhuna sama da 200 babu komai a ciki.

Kara karanta wannan

Kano: Abba Kabir ya kadu bayan bankado wata badakala, ya sha alwashin daukar mataki

Yan sanda sun kama hadimin gwamnan Kano da wani
Yan Sanda Sun Kama Hadimin Abba Gida Gida da Wani Kan Karkatar da Kayan Tallafi Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Laifin me suka aikata?

Jaridar Punch ta rahoto cewa wadanda ake zargin suna sauyawa shinkafa da da masaran da ke rumbun ajiyar a Sharada buhuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinan yan sandan ya ce:

"Tuni muka kaddamar da bincike don gano buhunan masara ko shinkafa nawa ne aka sauyawa buhu sannan aka siyar."

Gumel ya bayyana cewa za a gurfanar da wadanda ake zargin biyu a kotu bayan kammala bincike, rahoton The Guardian.

Abba ya nuna bacin ransa kan karkatar da kayan tallafi da wasu suka yi

Hakan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin ransa kan yadda wasu su ka karkatar da kayan tallafi a jihar.

Gwamnan ya bankado badakalar ce a ranar Asabar 2 ga watan Disamba yayin da ya kai ziyarar bazata wani babban sito a jihar.

Yayin ziyarar an gano kayan tallafi makare a cikin siton wanda aka ware don rage wa mutane radadin cire tallafi a jihar.

Kara karanta wannan

Dubun wasu hatsabiban 'yan bindiga 8 da suka addabi mutane ya cika a jihar Kaduna

Wata mazauniyar Kano ta nuna jin dadinta kan matakin da aka dauka na kama wadanda suka yi sama da fadi kan abincin da ya kamata al’umma sun amfana da shi.

Malama Zainab Ummi da ke zaune a Shagari kwatas ta ce:

“Wannan shine adalci kada a duba nasaba ko matsayin mutum duk wanda ya yi ba daidai ba a hukunta shi. Kuma hakan ya kara tabbatar mana mu kanawa cewa talakawa ne a gaban Abbanmu saboda bai duba cewa hadiminsa bane ya aikata laifin, don haka bari a kyale shi.
“Toh wai ta yaya ma za a ce kayan al’umma amma a samu mutum biyu su yi sama da fadi a kansa, ai hakki ma ba zai bar su ba. Idan ba rashin imani ba ka siyar da kayan tallafi, toh rashin imani mana wani ma yana nan ya kwana bai ci amma kai ka iya sacewa ka siyar.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: An kashe yan bindiga sama da 50 yayin da suka kai hari a jihar arewa

"Wannan mataki da aka dauka zai zamo izina ga sauran masu dabi’ar satar kayan gwamnati da zaran sun samu dama.”

Abba Yusuf ya cika alkawarin yan fansho

A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya kaddamar da biyan kudaden giratuti ga ma’aikata dubu biyar a jihar.

Abba Kabir ya ware naira biliyan 6 don bai wa ma’aikatan hakkinsu tare da wadanda su ka mutu a lokacin da su ke aiki, Legit ta tattaro.

An gudanar da bikin kaddamar da biyan kudaden ne a dakin taro da ke gidan gwamnatin jihar a yau Asabar 2 ga watan Disamba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng