Kano: Abba Kabir Ya Kadu Bayan Bankado Wata Badakala, Ya Sha Alwashin Daukar Mataki
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir ya bankado wani siton adana kayan abinci a Unguwar Sharada da ke birnin Kano
- Abba Kabir ya nuna damuwa kan yadda wasu tsiraru su ka karkatar da kayan tallafi don biyan buƙatar kansu
- Gwamnan ya sha alwashin zakulo dukkan wadanda ke da hannu a ciki tare da daukar mummunan mataki a kansu
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nuna bacin ransa kan yadda wasu su ka karkatar da kayan tallafi a jihar.
Gwamnan ya bankado badakalar ce a yau Asabar 2 ga watan Disamba yayin da ya kai ziyarar bazata wani babban sito a jihar.
Yaushe Abba Kabir ya bankado badakalar?
Kano: Gwamna Abba Kabir ya sanya yan fansho kuka yayin da ya cika musu alkwarin da ya dauka, ya koka
Yayin ziyarar an gano kayan tallafi makare a cikin siton wanda aka ware don rage wa mutane radadin cire tallafi a jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An samu kayan ne a wurin adana kaya a Unguwar Sharada inda mutane su ka juye kayan abincin tare da sauya masa mazubi don siyarwa a kasuwa.
Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan irin wannan aika-aika na mutane marasa tausayi da imani.
Wane alwashi Abba Kabir ya yi?
Ya sha alwashin daukar mummunan mataki kan wadanda aka samu samu da laifi.
Tuni ya umarci a yi binciken gaggawa don zakulo wadanda ke da hannu a cikin wannan aika-aika ta rashin tausayi.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya kaddamar da kayan tallafi ga marasa karfi bayan cire tallafin mai a kasar.
Mutanen da ake zargin sun juye masarar ce mai nauyin kilo 10 tare da dure ta a wasu buhunan don cin riba a kasuwanni.
Gwamna Abba ya kaddamar da biyan kudaden fansho
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya kaddamar da biyan naira biliyan shida don 'yan fansho a jihar.
Abba ya fara biyan kudaden ne a yau Asabar 2 ga watan Disamba a gidan gwamnatin jihar inda ya ce za a ci gaba.
Gwamnan ya koka yadda gwamnatin baya ta bar musu tarun basuka har naira biliyan 48 na 'yan fansho da giratuti.
Asali: Legit.ng