Murna Yayin da Gwamna Ya Sanar da Shirin Karin Mafi Karancin Albashi Ga Ma'aikata

Murna Yayin da Gwamna Ya Sanar da Shirin Karin Mafi Karancin Albashi Ga Ma'aikata

  • Gwamnan jihar Abia Alex Otti ya bayyana shirinsa na yin ƙarin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a jiharsa
  • Gwamnan ya bayyana cewa za a ƙara albashin ne duba da halin da ake ciki kan tattalin arziƙi a ƙasar nan
  • Gwamna Otti ya kuma musanta batun cewa ya ƙi tarewa a cikin sabon gidan gwamnatin jihar inda ya ce magabacinsa bai kammala shi ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya ce yana tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin inganta mafi ƙarancin albashin ma’aikatan jihar domin yin daidai da halin ake ciki na tattalin arziƙi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a daren ranar Juma'a a yayin da yake tattaunawa da manema labarai karo na uku a birnin Umuahia, babban birnin jihar, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamna Lawal ya sake tono zunzurutun bashin da tsoffin gwamnoni biyu suka bar masa tun daga 2015

Alex Otti zai kara albashin ma'aikata
Gwamna Alex zai kara mafi karancin albashi Hoto: Alex Otti
Asali: Facebook

Meyasa gwamnan zai yi ƙarin albashin?

A kalamansa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun fahimci cewa abubuwa sun ɗan yi wa mutane wahala. Muna tattaunawa da masu ruwa da tsaki don ganin yadda za mu inganta albashin ma’aikatan gwamnati daidai da halin da ake ciki na tattalin arziƙi."
"Muna aiki don ganin yadda za mu inganta ba kawai mafi ƙarancin albashi ba har ma da sauran abubuwa kuma nan ba da daɗewa ba zamu fitar da sanarwa kan hakan."

Gwamna Otti ya bayyana cewa manyan sakatarori da daraktoci da suka yi ritaya kwanan nan za su karbi bashin albashi da alawus-alawus ɗin da suke bi.

Ya kuma tabbatar da aniyarsa na biyan basussukan ƴan fansho kamar yadda ya alkawarta tun farko, rahoton The Punch ya tabbatar.

Gwamnan ya bayyana cewa ba ya zama a gidan gwamnati ne domin wanda ya gada ya ƙaddamar da sabon gidan gwamnatin jihar wanda ba a kammala ba, yayin wanda wancan tsohon ya kasance a lalace.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: An kashe gawurtaccen ɗan bindigan da ya hana jama'a zaman lafiya a arewa

"Magabacina ya ƙaddamar da ginin da bai kammala ba. Wannan yaudara ce mafi girma. Ba ya buƙatar ƙaddamar da shi." A cewarsa.

An Sanar da Lokacin Fara Mafi Karancin Albashi a Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta bayyana lokacin da za ta fara biyan ma'aikata saɓon mafi ƙarancin albashi.

Ministan yada labarai da wayar da kan al’umma, Idris Mohammed ya bayyana cewa za a fara biyan sabon tsarin mafi ƙarancin albashin ne a wataɓ Afirilun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng