An Tafka Asara Yayin da Mummunar Gobara Ta Tashi a Rukunin Wasu Shaguna
- An samu tashin wata mummunar gobara a rukunin wasu shaguna a yankin Ekpan cikin ƙaramar hukumar Uvwie ta jihar Delta
- Gobarar wacce ta tashi cikin tsakar dare a rukunin shagunan ta laƙume dukiya mai tarin yawa ta miliyoyin naira
- Gobarar dai ba a san musabbabin tashin ta ba sannan babu tabbacin cewa ko akwai wani da ta ritsa da shi a cikin shagunan
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - An ƙona kayayyi da kadarori na miliyoyin naira a wata mummunar gobara da ta tashi a yankin Ekpan, ƙaramar hukumar Uvwie ta jihar Delta.
Lamarin ya faru ne a kan hanyar NNPC Complex Road, kusa da shataletalen Ekpan da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Juma'a, 1 ga watan Disamban 2023, cewar rahoton The Nation.
Ba a iya tabbatar da ko gobarar ta ritsa da wani ba, saboda babu cikakkun bayanai kan gobarar har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, an tattaro cewa an tuntuɓi hukumar kashe gobara ta jihar Delta domin ceto lamarin, rahoton The Punch ya tabbatar.
A cikin wani gajeren faifan bidiyo wanda aka gani, an ga wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa suna ƙoƙarin ceto kayayykinsu kafin isowar hukumar kashe gobara.
Gobara ta babbake babbar kasuwar Kabba
An samu tashin wata gobara wacce ta jawo asarar miliyoyin naira a wani bangare na babbar kasuwar Kabba a jihar Kogi.
Gobarar ta lakume shaguna masu tarin yawa, yayin da ta bar 'yan kasuwa da mazauna yankin cikin tashin hankali, babu wanda ya iya shawo kanta.
Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 5 na Asuba, inda ta mamaye kasuwar tare da cinye shaguna masu yawa.
Mummunar Gobara Ta Shi a Jihar Kwara
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata mummunar gobara a babbar kasuwar Oja Tuntun da ke birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Gobarar wacce ta laƙume shaguna aƙalla biyar ta tashi ne cikin tsakar dare a ƙasuwar ta Oja Tuntun wacce ke da shaguna kusan 1,072, rumfuna 984 da manyan shagunan ajiyar kaya 27.
Asali: Legit.ng