Nasara Daga Allah: Sojoji Sun Kakkabe ’Yan Ta’adda 180 Tare da Kubutar da Mutum 234

Nasara Daga Allah: Sojoji Sun Kakkabe ’Yan Ta’adda 180 Tare da Kubutar da Mutum 234

  • A cikin mako daya, dakarun soji sun samu nasarar kakkabe 'yan ta'adda 180 tare da kama wasu 204
  • Shelkwatar tsaro ta kasa ta sanar da hakan inda ta ce ta kwato mutum 234 da aka yi garkuwa da su
  • Haka zalika 'yan ta'adda 91 sun mika wuya ga dakarun sojin da suka hada da manya da kananan yara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shelkwatar rundunar tsaro ta kasa ta yi bayani kan nasarorin da dakarun soji suka samu a makon da ya gabata.

Rahoton shelkwarar ya nuna cewa dakarun soji sun kashe sama da 'yan ta'adda 180, sun cafke 204 yayin da suka kubutar da mutum 234 da aka yi garkuwa da su.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun halaka dan bindiga, sun ceto malamin addini da wasu mutum 2 a jihar arewa

Sojojin Najeriya
A cikin mako daya, dakarun soji sun kakkabe 'yan ta'adda 180 tare da kama wasu 204. Hoto: Nigeria Army
Asali: Twitter

Daraktan watsa labarai na shelkwatar, Manjo Janar Edward Buba, a wata sanarwa ranar Juma'a ya ce an samu nasarar ne ta hare-haren sama da kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buba ya ce dakarun sojin sun kuma kwato manyan makamai 46 da manyan alburusai 148, da suka hada da bindigar AK-47 guda 30, bindigu kirar Josef Magnum.

Sauran sun hada da fistal hadin gida guda 12, gurneti guda ɗaya, makaman RPG, harsasan NATO guda 120, harsasai masu tsayin 7.62mm guda 364.

Yan ta'adda sun mika wuya

Sannan an kama motoci 34, wayoyi 64, babura 47 da tsabar kudi naira miliyan 1.5, da dai sauran su, Punch ta ruwaito, rahoton The Punch.

Daraktan ya kuma yi bayani cewa dakarun sun gudanar da samame a karamar hukumar Gulani, jihar Yobe inda suka damke masu garkuwa da hakar ma'adanai.

Ya ce 'yan ta'adda 91 da suka hada da maza 13, mata 35 da kananan yara 43 sun mika wuya ga dakarun a ranar 22 da 28 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin addinin musulunci da amarya da ango a Kaduna

Dan dako da baro ya kashe mai karbar haraji kan naira hamsin

A wani labarin, mazauna birnin Edo sun shiga tashin hankali bayan da wani mai dan dako da baro ya kashe wani mai karbar haraji.

An ruwaito cewa rigima ta hada su, lokacin da mai karbar harajin ya nemi dan dakon ya biya naira hamsin kudin tikiti, Legit Hausa ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.