Ban Taba Rokon Alfarmar a Saki Wanda EFCC Take Tuhuma Ba, Sarkin Ilorin

Ban Taba Rokon Alfarmar a Saki Wanda EFCC Take Tuhuma Ba, Sarkin Ilorin

  • Mai martaba sarkin Ilorin ya yi magana kan masu zuwa neman alfarma a hukumar EFCC a madadin masu laifi
  • Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya ce tunda aka kafa EFCC shekaru 22 da suka wuce bai taɓa zuwa rokon hukumar ta saki wani da take tuhuma ba
  • Ya ce masarautar Ilorin zata ci gaba da baiwa EFCC haɗin kai a kokarin hukumar da yaƙi da aikata laifuka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Sarkin Ilorin kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Kwara, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari, ya ce bai taɓa zuwa neman alfarma wurin EFCC kan wanda ake tuhuma ba.

Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji Ibrahim Sulu-Gambari.
Ban Taba Rokon Alfarmar a Saki Wanda EFCC Take Tuhuma Ba, Sarkin Ilorin Hoto: Punch
Asali: Facebook

Sarkin ya ce tun da aka kafa hukumar yaƙi da cin hanci EFCC shekaru 22 da suka wuce, bai taɓa zuwa ya nemi alfarma amadadin wanda ya taka doka ba, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Tsige Abba: Mambobin NNPP sun shiga tasku kan zanga-zangar da suka yi a Kano, APC ta yi magana

Basaraken ya bayyana haka ne yayin ta karɓi bakuncin shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙi zagon ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, a fadarsa da ke Ilorin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin ya ce tun da aka kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa, bai taba rokon alfarmar a saki wani wanda ake tuhuma da taka dokar kasa ba.

A kalamansa, Sarkin ya ce:

"Na yi haka ne saboda ba zan iya cewa gwamnati ta yi kuskure da ta ɗauko hanyar daidai ba. Masarautar Ilorin tana da zaman lafiya, duk masu tada hargisti zuwa suka yi."
"Masarautar Ilorin ita ce ƙofar da ke tsakanin arewa da kudancin Najeriya kuma ni ne mai gadin wannan ƙofa.

Sarki ya ba shugaban EFCC shawara

Ya shawarci Olukoyede ya nutsu ta bin doka da oda wajen gudanar da aikinsa kamar yadda ya yi alkawari yayin tantance shi a majalisar dattawa tare da yi masa addu’ar samun nasara a ofis.

Kara karanta wannan

"Cin zabe sai an hada da rauhanai" Shehu Sani ya yi wa Doguwa martani

Sarkin ya tabbatar wa shugabannin EFCC a Kwara cewa zai ba su goyo bayan 100 bisa ɗari wajen cimma nasara a yaƙi da masu aikata manyan laifukan almundahana.

An fara karancin tsabar kuɗi a Ondo

A wani rahoton Matsalar karancin takardun Naira ta ƙara kunno kai duk da umarnin CBN na ci gaba da amfani da tsoho da sabon Naira.

A jihar Ondo, bankuna sun kayyade adadin kudin da kowane kwastoma zai samu a rana saboda rashin wadatattun tsabar kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262