An Ga Tashin Hankali Yayin da 'Yan Bindiga Su Ka Sace Shahararren Malamin Addini da Wani Mutum 1
- 'Yan bindiga sun sace wani shahararren Fasto mai suna Kingsley Eze da wani abokinsa mai suna Uchenna Newman
- Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 30 ga watan Nuwamba da misalin karfe 8 na dare a kwanar Orieama
- An sace Faston ne a kauyen Umuekebi da ke karamar hukumar Isiala Mbano a jihar Imo
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Imo - Wasu mahara sun yi garkuwa da shahararren Fasto, Kingsley Eze a jihar Imo.
Maharan sun sace Kingsley ne da wani mutum daya a kauyen Umuekebi da ke karamar hukumar Isiala Mbano.
Yaushe lamarin ya faru a Imo?
Legit ta tattaro cewa Faston da aka fi sani da 'Father Ichie' shi ne shugaban cocin katolika na Michael a kauyen Umuekebi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tabbatar da cewa an kama Faston ne da mutumin bayan sun sauka a mota kirar Volvo yayin da maharan su ka kama su da misalin karfe 8 na dare.
Lamarin ya faru ne a jiya Alhamis 30 ga watan Nuwamba a kwanar Orieama da ke yankin.
Daya daga cikin mambobin cocin wanda ya boye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Wane martani 'yan sanda su ka yi a Imo?
Ya ce:
"Tabbas an yi garkuwa da Fasto Kingsley da Uchenna Newman a kwanar Orieama.
"An kama Faston ne a ranar Alhamis 30 ga watan Nuwamba da misalin karfe 8 na dare.
"Sun sace su ne yayin da su ka sauko a mota siyan kaya, maharan sun kuma yi fashi ga 'yan kasuwar da ke wurin."
Ya kara da cewa wannan abin bakin ciki ne inda ya yi addu'ar dawowar Faston lafiya, cewar Daily Post.
Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Henry Okoye bai yi martani ba har zuwa lokacin tattara wannan rahoto.
Mahara sun kai hari gidan kwamishinan zabe
A wani labarin, Wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari gidan kwamishinan zaben jihar Kogi.
Maharan sun kwashe fiye da mintuna 30 su na artabu da jami'an tsaro inda aka yi asarar dukiyoyi.
Wannan na zuwa ne kwanaki 20 kacal da gudanar da zaben gwamna a jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba.
Asali: Legit.ng