Kotun Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Abba Kabir da Ado Doguwa, Ta Umarci Biyan Diyyar Miliyan 25

Kotun Ta Yi Hukunci Kan Shari'ar Abba Kabir da Ado Doguwa, Ta Umarci Biyan Diyyar Miliyan 25

  • Babbar kotun Tarayya ta kori karar Gwamna Abba Kabir kan zargin kisan kai da ya ke yi wa Alhassan Doguwa
  • Kotun yayin hukuncin ta yi fatali da korafe-korafen yayin da ta umarci Abba Kabir ya biya diyyar miliyan 25 saboda kokarin bata suna
  • Gwamnan na zargin dan Majalisar da jagorantar 'yan ta'adda da cinna wa sakatariyar jami'yyar NNPP wuta a Kano

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta yi hukunci kan korafin Gwamna Abba Kabir a Kano kan zargin Alhassan Doguwa da ta'addanci.

Kotun ta yi watsi da karar inda gwamnan ke zargin dan Majalisar Tarayya, Alhassan Ado Doguwa da hannu a kisan kai a lokacin zabe.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar Abba Kabir da Ado Doguwa
Kotun ta raba gardama kan shari'ar Abba Kabir da Ado Doguwa. Hoto: Ado Doguwa, Abba Kabir.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Mai Shari'a, Donatus Okorowo yayin hukuncin ya umarci Abba Kabir ya biya diyyar miliyan 25 saboda ba ta suna da kuma jefa Doguwa cikin kunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Okorowo ya kuma umarci wanda ake zargin da kada ya sake shiga lamarin wanda ke kara a ko wane hali.

The Nation ta tattaro cewa an kama Doguwa a ranar 28 ga watan Faburairu a filin jirgin saman Aminu Kano yayin da ya ke kokarin tafiya Abuja.

Wane zargi ake yi kan Ado?

'Yan sanda sun bayyana cewa su na zargin Doguwa da jagorantar 'yan ta'adda su cinna wuta a sakatariyar jam'iyar NNPP a Kano.

Ana zargin Doguwa wanda dan Majalisar Tarayya ne da ke wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada a Kano da ta'addanci.

Yayin harin, rahotanni sun tabbatar da cewa mutane biyu sun rasa rayukansu inda dan Majalisar ya musanta haka, SolaceBase ta tattaro.

Kara karanta wannan

Rikicin shari'ar Kano: An kai karar Gwamna Yusuf Majalisar Dinkin Duniya, bayani ya fito

Sani Umar ya roki Abba Kabir kan shari'ar kotu

A wani labarin, mahaifin yarinyar da aka yi wa kisan gilla a shekarar 2019, Sani Umar ya roki Gwamna Abba Kabir kan sauya kotun shari'a.

An hallaka marigayiya Aisha Umar bayan an yi garkuwa da ita inda ake zargin Fadila Adamu da kisan.

Mahaifin yarinyar ya zargi cewa ana son sauya wurin shari'ar ne don jibantar da shari'ar da rashin adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.