Gwamnatin Tinubu: Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abun da Zai Faru a Watan Fabrairun 2024
- Primate Babatunde Elijah Ayodele ya shawarci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta inganta yanayin zamantakewa da tattalin arzikin Najeriya
- Primate Ayodele ya ce Allah ya nuna masa cewa za a yi wata gagarumar zanga-zanga a watan Fabrairun 2024 idan Shugaban kasa Tinubu ya gaza magance matsalolin tattalin arziki
- Legit Hausa ta rahoto cewa idan gwamnatin Tinubu ta cimma nasara a wannan sauye-sauye, zai taimaka wajen magance matsalolin kasuwanci, matsalar abinci, rashin ayyukan yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Primate Elijah Ayodele ya bukaci gwamnatin Bola Tinubu da ta inganta yanayin tattalin arziki a kasar.
Ayodele ya yi hasashen cewa idan har aka gaza yin haka, za a yi gagarumar zanga-zanga kan gwamnatin APC a 2023.
Ya kamata Tinubu ya magance tattalin arziki', Ayodele
Malamin addinin ya aika wannan sako ne ta shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayodele, shugaban cocin INRI evangelical spiritual ya ce:
"Akwai bukatar gwamnatin nan ta yi aiki tukuru ta bangaren tattalin arziki. Za a sami karin rudani zuwa watan Fabrairu 2024 kan abin da za a yi kan tattalin arzikin don inganta tattalin arzikin; don sanya tattalin arzikin ya zama mai girma kuma mai kyau.
"Akwai abubuwa da dama da ya zama dole gwamnatin ta yi don ta daidaita, idan ba haka ba, ina hango zanga-zanga na zuwa ta bangaren tattalin arziki da yanayin da kasar ke ciki.
"Wannan ita ce gaskiya, kuma magana ta gaskiya kenan."
Tinubu ya nada mashawarta kan tattalin arziki
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin sabbin hadimai 18 a ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima.
Tinubu ya amince da nadin masu ba da shawara na musamman da manyan mataimaka 18 domin aiwatar da kudirin gwamnatinsa a sassa daban-daban na tattalin arziki.
Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Shettima ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labarai na ofishinsa.
Asali: Legit.ng