Mazauna Gari a Kaduna Sun Tsere Yayin Da Sojoji Suka Bar Garin, ’Yan Bindiga Sun Farmake Su

Mazauna Gari a Kaduna Sun Tsere Yayin Da Sojoji Suka Bar Garin, ’Yan Bindiga Sun Farmake Su

  • Tashin hankali ya mamaye garin Maganda da ke Birnin Gwari jihar Kaduna bayan sojojin da aka girke a garin suka kwashe kayansu
  • Tsoro da fargaba suka mamaye zukatan 'yan garin inda suka fice daga gidajen su tare da barin amfanin gonakinsu don tsira da rayukansu
  • Jim kadan bayan tafiyar sojojin, rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun shiga garin tare da bi gida-gida suna karbar wayoyi da kudade

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kaduna - Mazauna garin Maganda da ke gundumar Magajin Gari ta III a Birnin Gwari, jihar Kaduna, sun tsere daga gidajensu bayan janye sojojin da aka girke a garin.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan garin sun tsere ne don tsoron farmakin 'yan bindiga wadanda ke addabar garin tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: An kashe yan bindiga sama da 50 yayin da suka kai hari a jihar arewa

Sojojin Najeria/Birnin Gwari/Jihar Kaduna/Yan Bindiga
Sakamakon fargabar hare-haen 'yan bindiga, mazauna garin Maganda ke Birnin Gwari jihar Kaduna sun tsere daga garinsu. Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Yadda 'yan bindiga suka farwa Maganda bayan tafiyar sojoji

Mazauna garin sun bayyana cewa jami'an tsaron da aka girke don kare mutanen garin, sun kwashe kayansu Asabar din da ta gabata, lamarin da ya jefa tsoro zukatan mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ismail A. Ahmed, tsohon kansilan gundumar wanda ya dauke matarsa da yaransa daga garin, ya ce 'yan bindigar sun far wa garin jim kadan bayan tafiyar sojojin.

Ya ce 'yan bindigar ba su fuskanci wata matsala ba, inda suka rinka bi gida-gida suna karbar wayoyi da kudade daga hannun mutane, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna Maganda sun hakura da dukiyoyinsu don tsira da rayukansu

Ahmed ya kara da cewa 'yan garin sun hakura sun bar gidajensu, amfanin gonakinsu da wasu kayayyakinsu don tsira da rayukansu.

"Na dauke iyalina mun gudu saboda yanzu muna cikin barazana. Mutane da dama sun bar amfanin gonarsu da wasu kayayyakin su.

Kara karanta wannan

Yan ta’adda sun bindige makanike har lahira, sun tafi da matarsa da yarsa a Nasarawa

"Ba a jima ba bayan tafiyar sojojin 'yan bindiga suka rinka shiga gida-gida suna karbar wayoyi da kudi daga hannun mutane."

A cewar tsohon kansilar gundumar.

Kotu ta hukunta matar da ta lakadawa mijinta duka a Kano

A wani labarin, wata mata da ta lakadawa mijinta dukan kawo wuka a Kano ta fuskanci hukuncin kotun majistire da ke Rijiyar Lemu.

Legit Hausa ta ruwaito cewa an gurfanar da matar ne mai suna Hafsa bisa zarginta da yi wa mijinta dukan tsiya kan zargin yana hira da 'yan mata a waya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.