‘Yan bindiga sun far wa kauyuka 10 a jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun far wa kauyuka 10 a jihar Zamfara

Rahotanni sun kawo cewa wasu yan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki wasa kauyuka guda 10 a jihar Zamfara inda suka sace shanu da dukiyoyin jama’a.

Kauyukan da aka kaima harin sun hada da Fura Girke, Majira, Kanawa, Yargeba, Takoka, Bargaja, Bundungel, Bantsa, Unguwar Matanda Makera.

Yan bindigan sun sace shanu iya san ransu da wasu dabbobin da dama sannan suka tafi da wani mutum guda.

Mazauna wadannan kauyuka kuwa basu ga ta zama ba domin kusan dukkan su arcewa cikin daji suka yi suka bar wa barayin garuruwan su.

‘Yan bindiga sun far wa kauyuka 10 a jihar Zamfara
‘Yan bindiga sun far wa kauyuka 10 a jihar Zamfara

Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Ibrahim Wakkala ya nuna juyayin sa ga mutanen wannan kauye sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta kawo wa mutanen jihar dauki.

KU KARANTA KUMA: Tsintsiya madaurinki daya: An gano Dolapo Osinbajo tana taya Aisha Buhari daurin dankwali

Sannan kuma ya yi kira ga jami’an tsaron dake aiki a jihar da su tsaurara matakan tsaro a jihar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labarai ku bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng