Jami’an Tsaro Sun Halaka Dan Bindiga, Sun Ceto Malamin Addini Da Wasu Mutum 2 a Jihar Arewa
- Jami'an tsaro sun yi zazzafan arangama da yan bindiga a yankin Toro da ke jihar Bauchi
- Yan sanda sun sheke dan bindiga a arangamar yayin da sauran suka tsere domin tsira da ransu
- Har ila yau, an ceto wani malamin addini da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su daga jihar Filato
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Jami'an yan sanda a jihar Bauchi sun kashe wani da ake zargin dan bindiga ne tare da ceto wani fasto da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su daga karamar hukumar Bassa ta jihar Filato a ranar Laraba, rahoton LIB.
Kakakin yan sandan jihar, Ahmed Wakili, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis, 29 ga watan Nuwamba, jaridar Premium Times ta rahoto.
Wakili ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mutanen da aka ceto sune Sunday Ayuba mai shekaru 40, Fasto Bala mai shekaru 50, Keziya Ayuba mai shekaru 50, wadanda aka yi garkuwa da su daga kauyen Raddi a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
“An tabbatar da cewa an yi garkuwa da wadanda abin ya shafa ne daga kauyukansu."
Yadda jami'an tsaro suka kashe dan bindiga da ceto mutum 3 da aka
An gudanar da aikin ne a kauyen Kadade da ke karamar hukumar Toro, jihar Bauchi a ranar Laraba.
Ya ce a ranar 29 ga watan Nuwamba da misalin karfe 1:00 na tsakar dare, wani Sabitu na kauyen Kadade a karamar hukumar Toro na jihar Bauchi ya kaiwa jami'an tsaro rahoton zuwan yan bindiga.
Mista Wakili ya bayyana cewa a wannan rana da misalin 12:30 na tsakar dare, wasu yan bindiga da ba a san adadinsu ba sun farmaki kauyen Kadade sannan suka hari gidan Yakubu Makeri na kauyen Yagi a gudunmar Rahama da nufin garkuwa da shi.
Ya kara da cewar:
"Wata tawaga ta jami'an tsaro da aka jona da ofishin yan sanda na Rishi da wasu yan banga biyu sun shiga aiki nan take sannan suka fafata da yan bindigar.
"Jami'an tsaron sun sha kan yan bindigar a arangamar da suka yi. Sakamakon haka, an kashe daya daga cikin yan bindigar yayin da sauran suka tsere don tsira da rayuwarsu."
Jawabin ya ce yayin arangama da yan bindigar, jami'an tsaron sun yi nasarar ceto mutane uku da aka ambata.
A cewar sanarwar, kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci DPO da ke kula da karamar hukumar Toro da ya inganta aikin sintiri a yankin.
Yan bindiga sun sheka manike a Nasarawa
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa tsagerun yan bindiga sun farmaki yankin Gandu na jami'ar tarayya ta Lafia a ranar Litinin, inda suka kashe wani makanike, sannan suka yi garkuwa da mata da diyarsa, rahoton LIB.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa maharan sun farmaki garin da misalin karfe 7:00 na yamma sannan suka yi ta harbi kan mai uwa da wahabi domin tsorata mazauna yankin.
Asali: Legit.ng