Majalisar Wakilai da Sanatoci Sun Fara Tafka Mahawar Kan Kudirin Kasafin Kuɗin 2024

Majalisar Wakilai da Sanatoci Sun Fara Tafka Mahawar Kan Kudirin Kasafin Kuɗin 2024

  • Kasafin kuɗin shekarar 2024 wanda shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gabatar ya tsallake zuwa karatu na biyu a majalisar wakilai
  • Shugaban masu rinjaye na majalisar, Julius Ihonvbere ne ya jagoranci mahawara kan kasafin a zaman yau Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, 2023
  • A ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, Shugaba Tinubu ya gabatar da kudirin kasafin wanda ake hasashen zai laƙume N27.5tr

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta fara aiki gadan-gadan kan kudirin kasafin kudin shekarar 2024 wanda zai laƙume kuɗi N27.5tr.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa kudirin kasafin kuɗin ya tsallake zuwa karatu na biyu a zaman mambobin majalisar wakilai ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Mambobi sun zaɓi sabon shugaban majalisar dokokin Jihar Nasarawa da mataimaki

Kasafin kuɗin 2024 ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.
Kasafin Kudin 2024 Ya Tsallake Karatu Na Biyu a Majalisar Wakilan Tarayya Hoto: HouseNGR
Asali: Facebook

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Julius Ihonvbere, wanda ya jagoranci muhawara kan muhimman abinda ke kunshe a cikin kasafin, ya yaba wa Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ihonvbere ya bayyana cewa tsaron ƙasa da kuma fannin ilimi za su ƙara bunƙasa duba da kasafin da aka ware wa ɓangarorin biyu masu matuƙar muhimmanci.

A kalamansa, shugaban masu rinjayen a majalisar wakilai ya ce:

"Najeriya zata samu tsaro duba da makudan kuɗin da aka ware wa ɓangaren sha'anin tsaro da kare al'umma."
"A matsayina na malamin makaranta na ji daɗi kuma na gamsu ga abinda aka ware wa ilimi na matakin farko. Ina da tabbacin ilimi zai gyaru a wannan karon."

Majalisar dattawa ta fara muhawara

Haka nan kuma majalisar dattawan Najeriya ta fara feɗe kasafin kuɗin 2024 a zamanta na yau Alhamis, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kasafin 2024: Jam'iyyar SDP ta shirya yin aiki da Tinubu don ci gaban Najeriya

Dukkan majalisun guda biyu na tarayya sun tafka muhawara kan abubuwan da ke tattare a kudirin kasafin, wanda ake fatan su amince da shi kafin ƙarshen 2023.

A jiya Laraba, Shugaban Ƙasa Tinubu ya gabatar da kasafin a zaman haɗin guiwa da aka haɗa mambobin majallisar wakilai da sanatoci wuri ɗaya.

Tinubu ya kashe wutar rikicin siyasar Ondo

A wani rahoton kuma Ana sa ran mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, zai rubuta takardar murabus da babu kwanan wata a jiki.

Wannan na ɗaya daga cikin matsayar da aka cimma yayin zaman sulhu da Shugaba Tinubu a karshen makon nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262