Basaraken Abuja Zai Biya Naira Miliyan 2 Kudin Fansar Matarsa da Aka Yi Garkuwa da Ita
- Masu garkuwa da mutane sun nemi naira miliyan 16 daga iyalan mata takwas da suka yi garkuwa da su a wani kauyen Abuja
- A ranar wata Litinin da ta gabata ne aka sace matan a lokacin da suke aikin gona, ciki har da matar sarkin garin
- Sai dai rahotanni sun bayyana cewa iyalan wadanda abin ya shafa na ci gaba da tattauna yiwuwar samun ragi kan wadannan kudade
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kuje, Abuja - Wadanda suka yi garkuwa da matar sarkin kauyen Gwambobe a yankin Kuje, Abuja tare da wasu mata bakwai, sun nemi naira miliyan 2 daga iyalan kowacce mace.
City & Crime ta ruwaito cewa a ranar waccan Litinin da ta gabata aka sace mata takwas ciki har da matar sarkin, a lokacin da suke aikin gona.
Iyalan matan da aka sace na tattaunawa da masu garkuwan
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin garin mai suna Shuaibu ya ce:
"Shugaban masu garkuwan ya kira wayar daya daga cikin matan da suka kama inda ya nemi naira miliyan biyu kudin fansar kowanne mace daya.
"Sai dai, wanda ke magana kai tsaye da su kan lamarin na ci gaba da neman alfarmarsu akan su rage kudin fansar."
Daily Trust ta ce har yanzu ba a ji ta bakin mai magana da yawun rundunar 'yan sanda ta Abuja, SP Ade Josephine kan wannan lamari ba.
Yan Boko Haram sun kashe mutum 11 a jihar Borno
A wani labarin, Legit ta ruwaito maku cewa akalla masu sana'ar itace 11 ne aka ce wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne suka sare kawunansu a karamar hukumar Damboa da ke jihar Borno.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin a kusa da Bale, wani kauye da ke a karamar hukumar Damboa.
A cewar majiyoyin ‘yan banga na yankin, an gano gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su a wata gona da misalin karfe 5 na yamma, Daily Trust ta ruwaito.
Majiyar ta ce mutanen na aikin hada gawayi, sa'ilin da 'yan Boko Haram suka yi masu zobe, inda aka kashe mutane shida nan take.
Asali: Legit.ng