Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Tarwatsa Bikin Auren Tsohuwar Budurwarsa Ya Girgiza Intanet

Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Tarwatsa Bikin Auren Tsohuwar Budurwarsa Ya Girgiza Intanet

  • Wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya ya nuna yadda wani mutum ya fusata bayan ya samu labarin cewa budurwarsa da ta haifa masa yaro za ta yi aure
  • An rahoto cewa ya farmaki wajen taron bikin a fusace sannan ya tarwatsa gaba daya taron yayin da aka gano amaryar taa sharbar kuka
  • An tattaro cewa amaryar ta ziyarci uban dan nata ranar jajiberin auren, amma wanda ya wallafa bidiyon bai fadi a inda abun ya far ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

An gano wata kyakkyawar amarya tana sharban kuka babu kakkautawa a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya.

Mutane sun taru a kanta, suna kokarin rarrashinta, amma sam ta kasa jin rarrashi yayin da ta ci gaba da kuka babu kakkautawa.

Kara karanta wannan

"Sun ishe ni da hayaniya", Wani mutumi ya farmaki coci da karnukansa 3, bidiyon ya haddasa cece-kuce

Saurayi ya tarwatsa auren tsohuwar budurwarsa
Bidiyon Yadda Wani Matashi Ya Tarwatsa Bikin Auren Tsohuwar Budurwarsa Ya Girgiza Intanet Hoto: Facebook/ilovecoupedecale.
Asali: Facebook

An shiga rudani sosai a wajen bikin musamman a lokacin da wani mutum da aka ce uban dan amaryar ne ya farmaki wajen babu shiri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da alama saurayin amaryar ya fusata da ganin cewa tana aure, kuma an rahoto cewa ya je wajen ne domin tarwatsa taron.

Wani rubutu da aka yi jikin bidiyon ya nuna cewa amaryar na tare da uban dan nata kwana daya kafin bikin.

Shafin Facebook mai suna I Love Couple Decale, da ya wallafa bidiyon bai bayyana a inda abun ya faru ba.

An yi mai take da:

"Mahaifin danta ya isa wajen don tarwatsa bikin saboda tana tare da shi ran jajiberin auren."

Legit Hausa ba za ta iya tabbatar da ko abun shiri bane, amma dai bidiyon ya yadu kuma ya samu mutum fiye da 400k da suka kalla.

Kara karanta wannan

Babu 'yancin yin haka, malamin addini ya gargadi masu tare hanya don yin salla, an yada bidiyon

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan bidiyon auren

Abdoul Aziz Savadogo ya ce:

"Karya na iya shafe shekaru dubu amma gaskiya a ta yi halinta cikin kwana 1! Ku zamo masu gaskiya da amana a soyayyarku."

Williams Emeric'k Diomandé ya ce:

"Allah ya ba mu hikima da fahimi don yin zabin da ya dace."

Amarya ta bata fuska a wajen bikinta

A wani labarin kuma, mun ji cewa jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wata amarya da ta ki taka rawa da mijinta a yayin shagalin bikinsu.

Saboda halin da amaryar ta nuna, mutane da dama da suka ga bidiyon suna ta tambayar ko dole aka yi mata don ta auri mutumin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng