Yanzu: Tashin Hankali Yayin da Jami’an NSCDC Suka Harbi Dalibai a Abuja Yayin Jarrabawa
- An zargi jami'an hukumar tsaro ta NSCDC da aikata manyan laifuka da cin zarafi
- Na baya-bayan nan da ya faru tsakanin jami'an NSCDC da daliban wata makarantar sakandare a Abuja, babban tarayyar Najeriya
- Harbin da jami'an NSCDC suka yi ya yi sanadiyar barkewar zanga-zanga da kamun wasu jami'an da ake zargi da aikata ba daidai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum
FCT, Abuja - Rundunar yan sanda ta kama tare da tsare wasu jami'an hukumar NSCDC guda uku a ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba kan harbin wasun dalibai biyu a makarantar sakandare na Life Camp.
Makarantar na a tsakanin yankunan Jabi da Gwarinpa a babban birnin tarayya, Abuja.
Lamarin ya afku ne da misalin karfe 11:29 na safe a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, mutane biyun da aka harba suna kwance a asibitin Gwarinpa suna jinya.
A halin yanzu ba a tabbatar da abun da ya haddasa harbin ba, amma dai jami'an na NSCDC sun kasance a makarantar ne domin bayar da tsaro yayin jarrabawar da ke gudana.
Dalibai sun yi zanga-zanga
Sakamakon harbin, wasu fusatattun dalibai sun farfasa motocin fatron uku mallakin hukumar NSCDC.
Da aka tuntube ta, Josephine Adeh, kakakin rundunar yan sandan babban birnin tarayya, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta bayyana cewa takwarorinta sun dawo da zaman lafiya a yankin da abun ya faru.
Adeh ta ce:
"Dalibai biyu da daka raunata suna samun kulawa a yanzu haka, kuma CP. Haruna Garba ya yi umurnin fara bincike kan lamarin."
A halin da ake ciki, hukumar NSCDC reshen Abuja bata yi martani kan ci gaban ba.
Duk wani yunkuri na jin ta bakin kakakin NSCDC reshen Abuja, Comfort Okomanyi, ya ci tura.
Jami'an NSCDC sun damke yan luwadi
A wani labarin, mun ji cewa jami'an hukumar tsaro ta sibil difens (NSCDC), sun daƙile wani shiri da wasu mutane suka yi na gudanar da auren jinsi a jihar Gombe.
Jaridar The Punch ta ce jami'an hukumar sun kuma cafke mutum 76 waɗanda ake zargin suna da hannu dumu-dumu a shirin gudanar da auren jinsin.
Asali: Legit.ng