Matasa Na Murna Yayin da Gwamnan PDP Ya Sanar da Biyan Dubu 10 Ko Wane Wata Ga Masu Bautar Kasa
- Matasa na murna yayin da gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya yi wa masu bautar kasa alkawarin makudan kudade
- Gwamna Fintiri ya bayyana cewa zai ci gaba da bai wa ko wane mai yi wa kasa hidima dubu 10 a wata don rage musu radadi
- Wannan na zuwa ne bayan takwaransa na jihar Taraba ya yi wa matasan goma ta arziki wurin bai wa ko wane dubu 245 a shekara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa – Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya yi alkawarin biyan masu bautar kasa a jihar dubu 10 ko wane wata.
Legit ta tattaro cewa gwamnan ya ce fara biyan alawus din zai fara ne daga watan Janairun sheakar 2024.
Nawa Fintiri zai rinka bayar wa?
Fintiri ya bayyana haka ne yayin da ake horas da matasan masu bautar kasa na rukunin ‘C’ kashi na biyu a yau Talata 28 ga watan Nuwamba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa dubu 10 da zai fara bayan kari ne kan dubu 20 da ko wane mai bautar zai karba bayan kammala yi wa kasa hidima.
Ya kara da cewa wannan wani shiri ne na gwamnatinsa don rage wa matasan radadin cire tallafin mai a kasar.
Wane alkawari Fintiri ya yi?
Gwamna Fintiri ya bukaci matasan da su yi amfani da damar da su ka samu zuwa jihar don cin gajiyar da kuma bunkasa kawunansu.
Har ila yau, Fintiri ya sanar da ba su kyautar buhunan shinkafa 50 da kuma shanu 10 da man gyada jarka 10.
Wannan na zuwa ne bayan cire tallafi da Shugaba Tinubu ya yi a watan Mayun wannan shekara, cewar The Nation.
Gwamna ya sanar da makudan kudade ga masu bautar kasa
A wani labarin, Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba ya saka murmushi a fuskar matasa masu bautar kasa bayan sanar da makudan kudade gare su.
Gwamnan ya ce ko wane matashi mai bautar kasa zai samu dubu 245 a shekarar da ya ke hidima a jihar.
Kefas ya bayyana haka ne a ranar Lahadi 24 ga watan Satumba inda ya ce ya yi hakan ne don rage musu radadin cire tallafi.
Asali: Legit.ng