NYSC ta saki sunayen yan bautar kasa 9 da suka nutse a ruwa a Taraba

NYSC ta saki sunayen yan bautar kasa 9 da suka nutse a ruwa a Taraba

Hukumar NYSC ta saki sunayen yan bautar kasa tara da suka nutse a kogon Mayo-Selbe dake karamar hukumar Gashaka na jihar Taraba.

A cewar jaridar Vanguard, sunayen da NYSC ta saki ya nuna cewa hudu daga cikin yan bautar kasar da suka nutse sun fito ne daga yankin kudu maso kudu, sannan hudu daga kudu maso gaban yayinda mutun guda ya fito daga yankin arewa maso yamma.

NYSC ta saki sunayen yan bautar kasa 9 da suka nutse a ruwa a Taraba
NYSC ta saki sunayen yan bautar kasa 9 da suka nutse a ruwa a Taraba

Legit.ng ta tattaro cewa sunayen mamatan sune Ucheonye Nkadi (jihar Delta), Ijeh Chile (jihar Delta), Irorobulor Blessing (jihar Delta), Solomon Miracle (jihar Edo), Ojimba Matilda (jihar Imo), Maduike Thelma, (jihar Imo), Onoduagu Arinze (jihar Enugu), Ezeamama Ifeanyi (jihar Anambra) and Adams Zipporah (jihar Kaduna).

KU KARANTA KUMA: Ba na adawa da amfani da katin zabe da na’urar tantance katin zabe - Buhari

Biyo bayan wannan mummunan lamari, daeakta janar na NYSC, Suleiman Kazaure ya dakatar da yan bautar kasa daga duk wani fita na shakawata ba tare da izini ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng