Shugaba Tinubu Ya Aike da Muhimman Saƙo Ga Majalisar Dattawa Kan Kasafin Kuɗin 2024
- Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wasiƙa zuwa majalisar dattawa kan kasafin kuɗin 2024 da zai gabatar gobe Laraba, 29 ga watan Nuwamba
- Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta sakon shugaban ƙasan a zaman yau Talata
- Bayan haka ne majalisar ta amince da buƙatar Bola Tinubu na yin zaman tare da mambobin majalisar wakilan tarayya a gobe Laraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana aniyarsa ta gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2014, na farko tun bayan hawansa kan gadon mulki.
Shugaban ƙasar ya sanar da shirinsa na gabatar da kasafin kuɗin idan Allah ya kaimu ranar Laraba (gobe), 29 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana ranar gabatar da kudirin a zaman haɗaka na majalisar tarayya a wata wasiƙa da ya aika zuwa majalisar dattawan Najeriya ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙar shugaban kasa a zaman sanatoci na yau 28 ga watan Nuwamba, Vanguard ta tattaro.
Majalisar dattawa ta amince da buƙatar shugaba Tinubu
Bayan haka ne, majalisar dattawan ta amince da buƙatar shugaba Tinubu na gudanar da zaman haɗaka da takwaorinsu na majalisar wakilai ranar Laraba.
Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan majalisar tarayya ta hannun sakataren yaɗa labarai, Dakta Ali Barde Umaru, ta sanar da cewa Bola Tinubu zai gabatar da jawabi ranar 29 ga watan Nuwamba.
Wannan ne karo na farko da shugaban ƙasar zai haɗa majalisun biyu a zama ɗaya kana ya gabatar da kasafin kudi tun bayan rantsar da shi a watan Mayu.
Legit Hausa ta fahimci cewa shugaba Tinubu ya ƙara kasafin 2023 da ke dab da karewa, wanda ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen tallafawa yan ƙasa su rage raɗaɗi.
Rikicin Shugabanci Ya Barke a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi
A wani rahoton Hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya haddasa sabon rikicin shugabnci a majalisar dokokin jihar Bauchi ranar Talata.
Kotun ta tsige kakakin majalisar da mataimakinsa, ta umarci INEC ta shirya sabon zabe a wasu rumfunan mazaɓu biyu.
Asali: Legit.ng