InnalilLahi: Allah Ya Yi Wa Diyar Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero Rasuwa

InnalilLahi: Allah Ya Yi Wa Diyar Sarkin Kano Marigayi Ado Bayero Rasuwa

  • Allah ya yi wa diyar Sarkin Kano Ado Bayero rasuwa a safiyar ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, 2023
  • An gudanar da jana'izar Hajiya Hauwa Ado Bayero a gidan sarkin Kano, da misalin karfe goma na safiya
  • Marigayiyar da aka fi sani da Hauwa Lele, kanwa ce ga sarkin Kano na yanzu da kuma sarkin Bichi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Rahotannin da muke samu na nuni da cewa Allah ya yi wa daya daga cikin 'yayan marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero rasuwa.

Allah ya karbi rayuwar Hajiya Hauwa Ado Bayero a safiyar ranar Talata, 28 ga watan Nuwamba, 2023 inda kuma aka gudanar da jana'izarta a gidan sarki.

Kara karanta wannan

An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

Hauwa Ado Bayero/Masarautar Kano
Hauwa Ado Bayero kanwace ga sarkin Kano na yanzu da kuma sarkin Bichi. Hoto: Ado Bayero Foundation
Asali: Facebook

Shafin masarautar Kano ya wallafa cewa an yi jana'izar ne da misalin karfe goma na safe, tare da rakiyar dumbin jama'a zuwa makwanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayiyar wacce ake kira da Hauwa Lele yar uwa ce ga sarkin Kano na yanzu Alhaji Aminu Ado Bayero da sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, kamar yadda shafin gidauniyar Ado Bayero ya wallafa.

Janar Kure da ya goranci murkushe Maitatsine a Kano ya rasu

A wani labarin da Legit Hausa ta ruwaito maku, kun karanta cewa Allah ya yi wa Janar Yohanna Yerima Kure (mai ritaya) rasuwa yana da shekaru 84 a duniya.

Janar Yohana Kure, kafin ritayarsa ya kasance babban kwamanda janar (GOC) na rundunar soji ta 82 da ke Enugu, da kuma rundunar sashen makamai ta 2 da ke Ibadan.

Bajintar Janar Kure a aikin soja

Kara karanta wannan

Abdul Amart da Rarara sun yi wa iyalan marigayi Aminu S Bono sha tara ta arziki

Kure, wanda ya taba rike mukamin darakta a sashen ayyuka da tsare-tsare na rundunar soji, ya mutu a Kaduna bayan doguwar jinya, Daily Trust ta ruwaito.

hi ne ya jagoranci dakarun soji wajen murkushe Maitatsine da jama'arsa a Kano a shekarar 1980 da kuma a Yola a shekarar 1982.

Ya mutu ya bar matarsa, 'yan uwa, da kuma 'yaya masu yawa, har da jikoki da sauran abokan arzuka.

Yaushe za a yi jana'izar Janar Kure?

The Guardian ta ruwaito za a gudanar da jana'izar binne gawar Janar Y.Y Kure a ranar 1 ga watan Disamba, 2023 a garinsa Kurmin Musa, karamar hukumar Kachia, jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.