‘Yan Najeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 2.6 a Sayen Data da Katin Waya Cikin Watanni 9

‘Yan Najeriya Sun Kashe Naira Tiriliyan 2.6 a Sayen Data da Katin Waya Cikin Watanni 9

  • Abin da ya yi ciwo wajen kira da hawa yanar gizo ta wayar salula da na’urorin zamani ya kai Naira tiriliyan 2.59
  • Daga farkon Junairu zuwa karshen watan Satumban shekarar nan, kamfanonin sadarwa sun samu tiriliyoyin kudi
  • Kamfanoni irinsu MTN da Airtel sun samu karuwar kudin shiga a Naira bayan sabon tsarin da gwamnati ta fito da shi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Adadin kudin da mutane su ka kashe a kan kamfanonin sadarwa ya kai akalla Naira tiriliyan 2.59 a cikin shekarar nan.

Bayanan da Punch ta samu daga kamfanonin MTN Nigeria da Airtel Africa sun nuna kudin sayen data da katin waya ya karu a 2023.

Waya.
Ana latsa wayar salula a taro Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Waya da yanar gizo sun ci N2.59tr

Daga watan Junairu zuwa Satumban bana, jama’a sun kashe kusan N2.6tr domin yin kira da kuma sayen data na hawa yanar gizo.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai batar da Naira Tiriliyan 27.5 a kasafin farko da aka yi a zamaninsa

An samu karin 32.57% na abin da aka batar a makamancin wannan lokaci a 2022 inda aka yi wa kamfanonin sadarwan ciniki N1.95tr.

Abin da ya jawo karin kashe kudin waya

Rahoton ya ce daga cikin abubuwan da su ka karin kashe kudin akwai karya darajar Naira da aka yi, wannan ya shafi kamfanin Airtel.

Haka zalika karin kudin da kamfanonin sadarwan su ka yi ya taimaka wajen karin da aka samu a watanni tara na farkon shekarar nan.

Yadda MTN da Airtel su ka samu kudi

A wajen saida data da katin waya, Airtel ya samu fiye da $1.41bn zuwa yanzu, idan aka yi lissafi a kan N461/$, kudin ya kai N647.71bn.

Kamfanin MTN ya samu karin 36.36% wajen saida data da karin 10.64% wajen saida katin kiran waya daga Junairu zuwa Satumba.

Kudin shigan $1.29bn da aka samu ya zarce N1tr idan aka yi lissafin canji a kan N777/$.

Kara karanta wannan

Sheikh Bala Lau ya yabawa Uba Sani kan 'inganta walwalar' mazauna Kaduna

Alkaluma sun nuna masu amfani da MTN domin hawa yanar gizo sun karu da 29.1% a shekarar nan saboda karuwar manyan wayoyi.

83.7% na masu amfani da kamfanin na MTN su na hawa yanar gizo ne da tsarin 4G. Ana sa rai nan gaba fasahar 5G za ta zagaya ko ina.

Kasafin kudin 2024

Ranar Larabar nan Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudin 2024 a zauren Majalisar Tarayya kamar aka samu labari daga majalisa.

Abin da zai fi jan hankali shi ne babu ko sisi da gwamnati za ta ware domin tallafin man fetur wanda Muhammadu Buhari ya cire.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng