Tashin Hankali: An Gano Gawar Shugaban Fulanin da Ya Ɓata Cikin Wani Yanayi a Arewa
- A karshe dai an gano gawar shugaban Fulani, Umar Ibrahim, wanda ya ɓata a yankin ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato
- Shugaban wata ƙungiyar Fulani ya ce an tsinci gawar ne a cikin wata tsohuwar rijiya tare da sojojin Operation Safe Haven
- Mamacin ya ɓata ne ranar Laraba yayin da ya je wurin matarsa da aka kwantar a asibiti a garin Mangu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Plateau - An gano gawar shugaban Fulani, Umar Ibrahim, wanda ya ɓata tun ranar Laraba da ta gabata a jihar Filato da ke Arewa ta tsakiya a Najeriya.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa an tsinci gawar mamacin ne a wata tsohuwar rijiya a ƙauyen Jokom da ke ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato.
Bayanai sun nuna cewa gabanin rasuwarsa, marigayin shi ne Ciroman Kumbun da ke ƙaramar hukumar Mangu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun rundunar sojin Operation Save Haven mai aikin wanzar da zaman lafiya a jihar, Kaftin Oya James, shi ne ya tabbatar da ci gaban.
Shugaban ƙungiyar fulani 'Gan Allah Fulani Development Association of the group, (GAFDAN)' ya ce mamacin ya ɓata ne daga fita daga asibiti da nufin siyo wa matarsa da aka kwantar abinci.
Yadda aka gano gawar marigayin
Garba Abdullahi, shugaban ƙungiyar GAFDAN na jihar Filato, ya yi bayanin yadda aƙa tsinci gawar marigayi shugaban Fulanin.
A rahoton Daily Post, Abdullahi ya ce:
"Ya ziyarci matarsa da ke kwance ba ta da lafiya a Mangu kusan ƙarfe 6:00 na yamma ranar Laraba, daga zuwa siyo mata abinci, aka neme shi aka rasa."
"Kwana huɗu ana bincike sannan aka gano gawarsa a wata tsohuwar rijiya kusa da asibitin. Sojojin Operation Safe Haven sun taimaka wajen gano gawar mamacin."
"Muna kira ga mambobin mu su zauna lafiya kada su ɗauki doka a hannunsu, mu ci gaba da zama masu bin doka da oda, jami'an tsaro na iya bakin kokarinsu."
Kisan dai wani babban koma baya ne a kokarin da hukumomin tsaro ke yi na maido da zaman lafiya a garin Mangu.
Dakarun Sojoji Sun Sama Nasara Kan Yan Ta'adda a Taraba
A wani rahoton kuma Dakarun sojojin Najeriya sun samu galaba kan miyagun ƴan masu yin garkuwa da mutane a birnin Jalingo na jihar Taraba.
Dakarun sojojin sun kai sumame ne kan maɓoyar ƴan ta'addan inda suka fatattake su tare da ceto mutum biyu da suka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng