Shugaba Tinubu Ya rantsar da Mutane 8 da Ya Naɗa, Ya Shiga Taro da Manyan Jiga-Jigai a Villa
- Bola Tinubu ya rantsar da sabbin manyan sakatarori takwas da ya naɗa kwanan nan bayan sun tsallake tantancewa
- Jim kaɗan bayan haka, shugaban ƙasar ya jagoranci taron majalisar zartarwa (FEC) a fadarsa da ke Abuja ranar Litinin
- Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, na cikin waɗanda suka halarci zaman
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da sabbin manyan sakatarori 8 waɗanda ya naɗa kwanan nan bayan sun tsallake matakin tantancewa.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa shugaban ya rantsar da su ne jim kaɗan gabanin fara taron majalisar zartarwa (FEC) a fadarsa da ke Abuja ranar Litinin.
Bayan kammala bikin rantsuwar, yanzu haka Bola Tinubu na jagorantar taron FEC wanda ya ƙunshi ministoci da wasu muƙarraban gwamnatin tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sunayen sabbin manyan sakatarori 8
Sabbin manyan sakatarorin da suka karbi rantsuwar kama aiki sun haɗa da, Ndakayo-Aishetu Gogo, Adeoye Adeleye Ayodeji, da Rimi Nura Abba.
Sauran sune, Bako Deborah Odoh, Omachi Raymond Omenka, Ahmed Dunoma Umar, Watti Tinuke, da kuma Ella Nicholas Agbo.
Tinubu ya shiga taron FEC
A halin yanzu, shugaba Tinubu na jagorantar taron FEC na wannan makon, wanda kuma mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya samu halarta.
Taron na yau Litinin ya samu halartar sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, da kuma shugabar hukumar kula da ma'aikatan FG, Folashade Yemi-Esan.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa kuma tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Honorabul Femi Gbajabiamila, yana cikin waɗanda aka gani sun shiga zaman.
Sauran mambobin FEC da suka samu halartar zaman sun haɗa da ministoci, da wasu manyan hadiman shugaban ƙasa da aka gayyata zuwa taron na wannan makon.
Idan baku manta ba, Gwamnatin Shugaba Tinubu ta sauya ranar taron FEC na mako-mako daga Laraba zuwa Litinin, kuma ta ce ba kowa zai rika zuwa taron ba sai wanda aka gayyata.
Matan NNPP sun yi zanga-zanga a Kano
A wani rahoton na daban Magoya bayan jam'iyyar NNPP mata sun mamaye hedkwatar yan sandan jihar Kano kan tsige Abba Kabir Yusuf.
Ɗaruruwan matan sun yi tattaki tun daga gidan Kwankwaso zuwa babban ofishin yan sanda suna jaddada cewa Abba suka zaɓa a watan Maris.
Asali: Legit.ng